Tofa wannan dare shine dare mafi mini arayuwar deezat bacci ya gagare tah haka tah zauna har gari yawaye tanah mai jimamin abinda yafaru jiya a club, tunda take ba ataba samun namiji daya taba yimata koda kallon banxa neh amman gashi yau Allah yakawo har wanda yaso yazagi ubantah, haka har tah tashi tayi sallan asuba jiki asanyaye, sai asannan bacci yayi awon gaba dah itah, Haneefah kuwa yau bayan tah tashi qin zuwa tayi dinning room taci abinci Dan tanah tsoron kada daddy yatambaye tah saidai kuma kash dole tah tashi taje tah gaida daddy, sabon kuka tafashe dashi dan itah kawai tsoron tah d'aya kada daddy yayi fushi dah itah, ji tayi takun mutum akusa dah part dinta sauri tayi tah share hawayen tah bilal neh yashigo dah sallama Anty Ina kwana, lafiya Katashi lfy little bro, eh Alhamdulillah lovely Sis daman daddy neh yace ki sauko muci abinci tun daxu muke jiran ki, laa kuyi haquri wlh yau natashi babu apatite neh so bansan kunata jira nabah, muje kaji tashi tayi tah riqe shi sannan suka nufi dinning room din... Nan suka tarar dah KowA dah KowA itah kawai ake jira, Ina kwana daddy tace tanah mai sunkuyar dah kanta, sanna tanufi mummy tace mummynah ina kwana tareda zama a kujeran kusa dah mom, daddy neh ya Kalle tah yace " Aw princess abin er sankai ce daman lallai mah wato kusa dah mom naki zaki zauna koh shikenan nayi fushi, haba daddy kasan ai nafi sanka akan mummy fah, Aw yanxu kuma dadin baki kikewa daddyn naki, duk dariya sukayi, Khaleed neh yace " mom & dad ni bakuma bari na karbi girma nebah, koh gaishe ni batai bah fah, laa yaya Khaleed ina kwana sowwie na sha'afa neh fah, dukkan su dariya suka soma yi sosai, sannan Haneefah tayi serving dinsu chip nd plantain with sauce& fried egg, tea tahada musu dukkan su daddy neh yasa matah albarkah sannan sukayi Bismillahi tareda fara bawa cikinsu haqin sah, bayan sungama neh kowa yayi Alhamdulillah tareda miqewa dan barin dinning room din daddy neh yace princess ki tsaya inada magana dake, mamace tace dah Haneefah toh kaddai akwace min miji Kai mummy nina isa dariya mama tayi tawuce, Khaleed neh yamike yace Sis ince dai bah aure kika cewa dad kinaso bah, fuskan tah tayi saurin rufewa tace haba ya Khaleed nifa babu ruwanah dah maza, hmmmm kamar gaske duk kyaun nan naki cewar Khaleed, daddy neh yace kaxo dah shirmen kah koh Khaleed kai yanxu gashinan duk kah kasa aure saidai kawai kadinga damun matata dah kukan yunwa kullum tana maka girki, daddy nifa yaro neh, ficce min daganan mara kunya kawai, dariya khaleed yayi sosai sannan yabasu waje, Haneefah kam duk abinda suke dariya takeyi amman bata Kai zuci bah duk hankalin tah yah tashi akan abinda xata fad'awa daddy Dan tasan daddy bayasan cutar dawani gashi kuma tasan sun cuci su ikbar, hawaye neh yake shirin sauko matah tayi saurin gogewa daddy yakalle tah yace princess lafiya kuwa? Eh daddy bakomai fah, aa ai GA damuwa it's written all over your face kuma kice min babu komai, haba princess yanxu akwai abinda xaki iya boyemin daman, daddy kayi haquri wani abu nah tuno mai ban tausayi Wallahi, toh kinga tabbata bakida damuwa? amsawa tayi dah eh, toh daman akan er gidan Alhaji Ahmad neh Dije, dam taji gabanta yayi mugun fadiwa, email daddy metayi? A'a Princess bakomai daman sonake naji abinda ya had'a ku jiya dah ita, laa daddy bkomai ai, aikuwa indai qarya zakimin yanxu Zamu bata dake nasan halinki kuma nasan bah deezat, menene? Kifada min Dan nah tabbata akwai abinda yahada ku, daddy kasan ai deezat dah tsira kawai sabani muka Dan samu fah ita, ai kasan halin tah rashin haquri yayi matah yauwa, hakane princess amman naso ki fada min ASALIN abinda yafaru, shikenan toh, kije har taxo Zatah tashi daddy yaja dogon numfashi yace My Princess, Na'am zauna Kiji........... Mhiss β~hal 08094275077 [12/02 21:29] Ummuhaneefah: SALIN RAYUWA ☣131↗135☣ Novel writer ♀ mhiss β~hal Dedication of page goes to my dear Mass Communicator, Pls ayi karatu Allah yabada sa'a. Love yeah Dan Allah Dan Annabi fans Kuyi min Uziri wlh wlh wlh I am too busy I dnt even have enough time 4 myself but Pls just know that my love and care for you all are sincere Haneefah zama tayi tah sunkuyar dah kanta, daddy yafara magana dah cewa "kinga tun kina qarrama kuke qawance dah Dije, mukuma muke zumunci dasu, toh amman saidai ni kinsan banasan qawancen ku sosai badan komai bah sabida halaiyar Dije, kinga yarinyar nan tunda kuka fara qawance, agida neh kawai baki canxa bah amman halaiyar ki awaje banajin dadi shi domin so dayauwa mutane kan kawo min qarar ki, atimes har abokai nah kike wucewa babu gaisuwa, duk kema tah koya miki aqidar tah nah wulaqantah jama'a ke kuma tunda kinsan baki isa kimin shi acikin gida bah, sai kikeyi awaje, ita kuwa Dije koh en gidan su bata saurara wa bah, harta babantah so dayauwa yake kawomin qarantah, kuma nakam matah fad'a amatsayina nah mahaifinta nabiyu, amman saidai kash wanan d'iyar tafita daban acikin AL'uma, fatanah dai kullum shine Allah yashirya manah ita, princess Inaso kisan cewa Allah bayasan mutum mai wulaqantah Dan Adam, so Dan Allah kada naqara jin ance kin wulaqantah wani koh wata, shikenan tashi kije Allah yamuku albarkah baki daya, daddy nagode sosai kuma Insha Allah nadaina, itama deezat din zanyi qoqari akantah akan hakan, yauwa princess toh shikenan, tashi tayi tabar gaban daddy dakintah tah nufa taje tah kwanta tunani tah shiga yi yanxu idan haqqin su ikbar yakamatah fah, wanka tah shiga tah shirya dan fita zuwa unguwan..... Deezat yaukam shuru babu anushuwa Kira neh yashigo matah, ilham ce tayi mamakin hakan sosai dan kawai saidai haduwar clubbing amman sunada digits din juna kawai basa contacting juna neh, sai lokacin club, picking tayi tasa akunne, ilham ce tace yakike babe yajiki jiya kinbar club so early, Uhm m awk Tam kihau facebook yanxu if u are less busy akwai wani post dah nakesan kigani, awk tnx bye, ganin babu abinda takeyi yasa tah hau facebook post din tah duba tah cigaba dah chatting sama-sama, Almustapha neh kwance akan gado, riqe dawaya yanata chatting tunawa yayi dah deezat yace, definitely her user name wil exactly yanda yake a bored din, searching yayi in just a blink of an eye yayi resulting dah deezat har uku nah farkon yaduba nan yayi tozali dah pics din deezat harda Wanda tayi a club daidai parking spot natah, request yayi clicking, sannan yacigaba dah kallon pics dintah, Deezat request tah gani daa kamar baxatayi accepting bah kuma saitaga double name kasan cewar tanasan double name sosai, Almustapha Abbas Mustapha, wow tace tayi accepting, Almustapha qarar notification yaji, dubawa yajeyi to his surprise yaga har tayi accepting "mamaki yayi sosai yace so this girl is so cheap, Almustapha neh yace Salam alaiki, Deezat tah gani tah share azuciyar tah tanah cewa wannan wawan yadauka ni am so cheap hakan nan sabida yaga nayi accepting dinshi without waste of time, mtsww tsaki Taja tah cigaba can numban yadinga damun tah hakan nan tah duba taga yayi posting matah funny videos Wanda yasata dariya sosai har taji tah dan samu relief akan damuwan tah, sai tayi deciding tah amsa sallamar sah, amsawa tayi, Almustapha: y kk Deezat: gallant of cax Almustapha : nice hearing dat frm U Deezat : kkk Almustapha : Hmmmm wannan Kkk hakan KAmar kin gaji dani Deezat : Chab da fah ai Kai bah qanin Ubana baneh Almustapha : Hmmm koh kin kyauta xakiyi bayani neh Deezat : kayi kadan fah Almustapha : Tam shikenan ki huta Deezat : daman kullum Cikin Hutu nake Almustapha : ke bye dnt hav tym 2 waste Deezat : nice Keh? Almustapha kin dade bakiyi fushi bah Deezat : lallai wuyan kah ya isa yanka Almustapha : saida sallah agidan ku Deezat : what? Almustapha : bye kkkk Mhiss β~hal 08094275077 [13/02 09:04] Ummuhaneefah: SALIN RAYUWA ☣136↗140☣ Novel writer ♀ mhiss β~hal Dedication of page goes to Xeesarkie Abangaren su ikbar kuwa rayuwa tah daidaitah kullum suna rayuwar su cikin jindadi Safia har tah shiga sch tah fara daga Jss2 sakamakon cin interview din Jss 2 dah tayi, yanxu kam basuda watah matsala Dan Allah yarufa musu asiri, ikbar dai Aisha tela tah dame shi dah Kira kullum saita kirashi, GA morning & night messages, shikam yakasa gane nufin hakan amman har yasaba duk dah cewa baya sakewa dah hakan, haka take kiranshi su gaisah tah tambaye sa su mama, shima har yafara sabawa dah hakan Yayan tambaye tah yatake dah aikin tah, Safia kam yanxu tayi bestfrnd a sch sunanta yasmeen sukan gaisawa tah wayan mama, Haneefah kuwa tunda tah bar unguwan su ikbar babu nasara hankalin tah yayi dubu atashi gashi takusan komawa London Kyla tah shiga yi key tafito dashi tah nufi gidan dah daddy yabata dan tah huta, Mama bara naje garden kinji, toh Safia kada kidade Nafisan naji ku kusa dani kinga ai Kece autah, Kai toh mama ai garden din yanah cikin gida, eh duk gnash hakan amman dad'an nisa dah nan ai koh kiranki nayi daga nan abu daya neh xaisa ki iyaji sabida bamuda yauwa cikin gida, toh mama the garden is so extremely beautiful shiyasa nakesan zuwa, toh kije Amman kada kidade, toh tace cike dah murna tah nufi garden tanah Cikin garden tanah shaqar kamshin flowers din tanah musu hoto, kawai taji qara kamar ana bude qofa, tah dauka gidan maqota neh cax duk basu San dah qofa awajan bah daidai kuma qara yaqi tsayawa ji tayi kamar qofa yabude kuma taji taken qwas-qwas dam gaban tah yafadi, shikenan yau aljana xatah cinye ni baxan qara ganin mamanah dah yayana bah, kuka take sosai babu sassauci, Haneefah taxo shigewa cikin daqi taji kamar kukan mutum amman silently garden din dah tah gani abuse neh yasa tanufi qofar, Tanah zuwa taga kamar atampha tah ragar qofa hakan tah qarasa tah shiga ciki shuru tayi dah ganin Wata kyakyawar yarinya sai hawaye takeyi Kaman bah gobe, Safia kuwa tagama razana ihu tah kenan yi amman tanah tsoron kada hankalin mama yatashi kawai Addu'oi tasoma yi duk wanda yaxo matah kawai yi take, tagadai Haneefah kallon tah take dakyar tah iya cewa Dan Allah aljana kada ki cinye ni wayyo nashiga uku daman saidah mama tace baxanxo bah, Haneefah kam ai Safia sha'awa tabata jitayi dama taxama real lilsis natah, murmushi tayi tace kiyi haquri bah aljana bace, daman nakarbi hayan gidan neh Dan Hutu toh meshi ashe ya siyar bai fadamin bah Haneefah tayi matah qarya dan tasan maybe daddy yamanta yace matah yasiyar d'aya karbi key yabata wani, haneefah tah kalli Safia sannan tace amman yanxu kidan bari nah huta Saina tafi baxan qara dawowa bah in fact Xan baki mukullin back door din kawai dan kitabbatar dah hakan, Safia shuru tayi tanah kallon tah sai hawaye take itakam har zuciyar tah tsoro takeji sosai, Haneefah ce tah matsa kusa dah ita dagudu Safia taja baya, Haneefah tace Dan Allah kidaina gudu nah wlh baxan cutar dake bah tanah fadin hakan hawaye nabin kuncin tah, Safia shuru tayi sannan tace toh wace ke, Haneefah tah amsa matah dah mutum kuma wacce baxata cutar dake bah, Haneefah kuma matsawa tayi kusa dah Safia tah riqe hannun tah Safia cikin tah har qara yake dan tsoro, dariya Haneefah tah sakar matah dan taga alamun tsoro atattare dah itah sannan tace haba dear sis ai yanxu kinga ni bah aljana bace amman kike tsorona, toh shikenan nabar muku gidanku sai anjima, Safia tayi saurin riqe tah tace toh zoki huta manah saiki tafi, dakin farko Haneefah tah shiga tafada kan gado, Itakuwa Safia tanah tsaye sai kallon tah take fridge tanufa nah dakin taga Bkomai ciki gashi batasan mama tasan dazuwar Haneefah, dabara ce tafado matah, tace ina zuwa Kixauna kada kibar nan banasan aganki, ciki tah shiga taga babu KowA a parlour mama tanah dakin tah maybe mah bacci take, hamdala tayi tawuce ciki dah gudu fridge taje tah debi chocolates dah cakes dah big mister yasai matah, sannan tah dauki lemu dah ruwa takoma wajan dasaurin tah, shiga tayi tanah haqqi sosai hakan yasa tafara tari Haneefah tayi saurin tashi tareda bude ruwa tabata abaki, sanan tah rungume tah tanah bugun bayanta ahankali, shuru duk su biyun babu wanda yayi magana cikinsu, KowA tunanin sah yake, Haneefah cewa take inama bah ita kadai ce mace bah tanada qanwa, itama Safia cewa take inama yaya ikbar macece tanada yaya, Haneefah ce tah janye tah tace Sannu koh ruwan ya ishe ki, Kai tah gyada alamun Eh sannan tace anty ga wannan kici, cake tah bude matah dah chocolate sannan tabude matah lemu, Haneefah tace aa bakina tsoro nabah kince nabar muku gidanku, ai tafiya xanyi baxan ciba, idon Safia yaciko sosai dah hawaye tace wasa fah nake mama tace "baqon kah annabin kah, dariya Haneefah tayi tace toh saidai muci tare........ Mhiss β~hal 08094275077 [13/02 12:04] Ummuhaneefah: SALIN RAYUWA ☣141↗145☣ Novel writer ♀ mhiss β~hal Dedication of page goes to ASALIN RAYUWA NOVEL FANS GROUP, I love you all ur comments & Allah keeps me goin Cakes dah chocolates din suka shiga ci tare ahankali babu Wanda yace dah wani komai, Haneefah ce tace kibani labari kinji Sis, Safia tayi shuru tarasa mexata ce kawai sai tace anty daga ina kikazo nan, haneefah dah tah tuna wahalan dah tasha wajan neman su ikbar amman batayi nasara bah, tafashe dah kuka sosai, Safia sosai taji tausayin tah itama kukan tafara dankwalin tah tazaro tafara gogewa Haneefah hawaye, tanah cewa anty bakida gida neh toh kada kidamu Xan boyeki anan kuma zan dinga Kawo miki abinci kinji? murmushi haneefah tasaki tace a'a Sis inada gida kawai wasu mutane nake nema wanda nayi musu laifi, inaso nagansu suyafe min kuma inata zuwa gidansu amman bana ganin su, toh Anty kiyi haquri kinji roqi Allah yabayyana miki su kinji, Kai Haneefah tah Kyada tace toh, anty bakici dayauwa bah muci toh, cigaba dah cin abincin su sukayi bayan sungama sunyi Hamdala Safia tacewa Haneefah xatah shiga kada Mama tah nemeh tah, "anty ki kwanta kiyi bacci xanxo nah tashe ki anjima, godiya Haneefah tayi sannan tabi lafiyan gado, Safia nashiga ciki dah paranti ahannu tah hangi corridor nah dakin mama abude kitchen tawuce taje tah ajiye Sanan tanufi daakin Mama tah tarar tanah sallah zuwa tayi tace mama bacci kikayi nadawo naga kinbar parlour Eh wlh Safia jekiyi sallan LA'asar kixo muyi girki Kafin yayanki yadawo yace yatafi biyan Idi mai Shago kudinsa, sallah Safia take tayi suka shiga kitchen dah mama tuwon shinkafa miyan taushe wanda yaji kayan hadi sosai dah nama suka tsara sai 5:30pm suka kammala, Safia warmer tah dauka tah zubawa Haneefah ishashe, tanufi dakin tah ta ajiye sabida mama tanah falo, tah dawo tah zauna itah dah mama kallo suke a main parlour, Safia kuwa tunani take tayaya xataje tah tashi anty ga lokaci yanah tafiya har ankusan magrib, haka take zaune tanah kallo amman hankalin tah baya wajan har aka Kira sallah mama tamiqe tanufi dakintah dan tayi Sallah, aida gudu Safia taje daqi tah dauqi warmer tawuce dakin dah Haneefah take, ahankali tasoma tashin tah, farkawa tayi "Alhamdulillahi lazee ayana ba'ada ma amatana WA ilayhin nushoor'' haneefah tace tareda miqewa, sallah taji ana Kira tah zaro ido tace sis qarfe nawa, Safia tace anty magrib yayi fah kiyi haquri ban tashe ki dawuri bah akasi aka samu, bakomai Haneefah tace tah tashi tah gyara gyalen tah, tah riqe hannun Safia tah bata key din tace ga key din as promised baxan sake dawowa bah, Safia idanta yaciko tace anty banda yaya Pls ki tafi dah key din kidinga dawowa kawai let's keep it a secret Pls, sosai Haneefah taji dadi at least tasamu er uwa, toh tace tareda yimata murmushi bara natafi gobe xan dawo kinji, toh Safia tace tare dah miqa matah warmer gashi abincin Daren ki anty, haneefah taqi karba amman Safia tayi insisting har Haneefah tah karba tayi murna sosai tareda yimata godia, Safia itama tayi murmushi takaita har back door sannan tace anty promise u will come back, I promise dear go in Pls, OK take care komawa tayi cikin gida tayi dakinta tayi alwala yayi sallah..... Almustapha kwa kiran Abdulaziz yayi yagaya masa komai yanda sukayi dah deezat, Abdulaziz yace guy amman kayi daidai kada kah dinga raga matah idan bahaka bah zatah raina kah, eh ai daman yanxu mah tun safe banqara matah magana bah sai later idan nayi sallan isha zan matah magana cewar Almustapha, haka suka dan taba hira sannan sukayi sallama yakashe wayar, ya tashi ya daurawa shida Mal Abbas dinner kafin sallan isha Mhiss β~hal 08094275077 [14/02 21:04] Ummuhaneefah: SALIN RAYUWA ☣146↗150☣ Novel writer ♀ mhiss β~hal Dedication goes to ASALIN RAYUWA NOVEL FANS GROUP u guys are unique Ikbar yakai awa uku a unguwar su yanah jiran Idi Mai Shago jiranshi yayi sabida ance masa kasuwa yaje yakusan dawowa, hakan yasa yadan lalleqa maqotan su KowA yaga alamun canji atattare dashi amman sam bai maida hakan abin kuri bah Dan yasan yin Allah neh, bayan yafito daga sallan magriba neh ya Iske idi nashigar dah kaya cikin shago qarasowa yayi gabansa tare dah yimasa sallama, amsawa yayi yanah mai kallon mamaki gare ikbar, Hannu yabasa suka gaisa, wai yaushe kaxo daman kananan amman kah guje mu, dariya ikbar yayi sannan yace wlh ai nadade ina jiranka, wai kaje kasuwa shine nayi zaman jiran kah, Allah Sarki toh ya rayuwa? rayuwa Alhamdulillah sai godiya ikbar ya amsa atake, daman naxo biyan bashi neh wanda nah dinga karba wajan kah, tirqashi Eh toh gaskia banyi mamakin hakan bah dan daga ganin yanayin shigarka nasan abubuwa sun daidaita, shago yashiga yadauko littafin bashi bayan sun bude suka tarar bashin su ikbar yakai dubu goma shatakwas dah dah naira hamsin, idi Mai Shago yace nah yafe hamsin din Kaban shatakwas din kawai, dubu ashirin ikbar yaxaro ya miqa masa yace yasaiwa ersa abu dah canji, sannan yace "sakallahu khairan FIL duniya wal akira wal Jazakkallahu BIL Jannah Mal. idi, cike dah murna idi Mai Shago yakaranta Addu'an wanda aka biya bashi " Baarakallahu laka fee'ahlika WA Maalika, innama jaza'us salafi hamdu wal'adaa, ikbar yaqara yiwa idi godia, haka idi yace bakomai Allah yaqaro budi yarako shi hanya, suna cikin tafiya neh idi yace Hmmmm rayuwa kenan Allah yasah mudace yanxu dah kukabar unguwan nan kamar baku taba rayuwa cikin tah bah, murmushi ikbar yadanyi sannan yace ai ribar riqe Allah kenan haka sukayi sallama suka rabu abakin titi, ikbar yanah qoqarin tsayar dah Cabman kenan taji horn agaban shi, dubawa yayi yaga ashe Aisha tela ce, sannu fah ashe kaine shiga nayi dropping dinka pls, ikbar yace A'a Cab xai dauka zuwa gida, haka tayi insisting, murmushi yayi ya shige tareda yin sallama, amsawa tayi tanata kallon sah asace har suka isa gida, yayi matah godia sosai sannan ya tambaye tah ya akai tagane shi aduhu, dariya tayi azuciyar tah tanah cewa yaxa ayi taqi gane farin cikin tah, sannan tace masa ai duhu baiyi bah sosai shiyasa, sallama sukayi yashige tah wuce... Deezat kuwa tun chat din dasuka yi dah Almustapha taga he doesn't care about who she really is neh yasah yayi deciding bishi ahankali cax batasan abinda yafaru a club ya maimaita kanshi, tanah mai jimamin abin sosai, ahaka har akayi sallan isha bayan tayi sallah neh Afram tah shigo daqin tah dah abinci a warmers, sallama tayi deezat tah amsa bah yabo bah fallasa, sis yau tin safe shuru abinci nakawo manah muci, deezat taga ashe babu abinda yafi Dan uwa despite the fact that kullum takewa Afram wulaqanci tareda quntata matah amman still tajita shuru tabita har daqi, tnx dear tace Afram tayi mamaki sosai amman bata nuna hakan bah serving dinsu tayi suka fara ci tare, haka tadan samu taci sosai, bayan sun gama neh sukai hamdala plates din dah coolers Afram tayi waje dasu, deezat kwa facebook tahau nan tah tarar dah Almustapha online har yamata magana, amsa sallamar sah tayi tah share shi can yace matah haba sis yanxu fishi kike dani babu kyau fah blood is thicker than water, dariya abin yabata sosai tace: Hmmm tayaya naxama sis dinka bayan Kai stranger neh, yace: u remain my sis forever nd i will protect you always Words dinshi sun birge tah sosai haka kawai taji yakwanta matah arai tace: hmmmmmm sure? toh Allah yasah bah aljani baneh Almustapha dariya yayi afilin yace saidai kafi aljani yace: Hmmm haba sis yazaki cemin hakan dan nadamu dake gaskia saikin bani haquri tace: abinda banah yi kenan in fact ban tabayi bah yace: what? I juz cnt bliv it ai it doesn't make any sense ace bakisan idan kinyi laifi bah kibada haquri mtwss tace: what amman yanxu kace xakayi protecting dinah amman gashi u re already tired of me, yace: kinga bye banda tym to waste akanki bakiyi deserving protection Dinah bah gaskia Mhiss β~hal 08094275077 [14/02 21:04] Ummuhaneefah: SALIN RAYUWA ☣151↗152☣ Novel writer ♀ mhiss β~hal Dedication goes to my lovely Sis deejah radio yar'adua tah, missing U is nt my plan juz couldn't help myself out, pls com bak home Sauka yayi bai qara yimata magana bah, tofa yanxu kam batasan wani yaqara matah wulaqanci hakan yasah jikin tah yayi sanyi, shuru tayi tarasa abin yi gashi har zuciyar tah batasan tabashi haquri, haka har bacci yayi awon gaba dah itah Haneefah kuwa tah dade bata tsinci kanta cikin farin ciki irin nayau bah, sai ayanxu tah dad'a yiwa Allah godia dah tah canxa hali, yanxu dah tananan dah wulaqancin tah dabaza su jitu dah Safia bah murna take sosai tasamu Sis abincin tah tadauko taci sannan tabi lafiyan gado.... Ikbar kuwa tunda yashiga gida suka gaisa dasu mama yadan xauna a parlour, bayan yaci abinci ciki yashige dawuri sakamakon gajiya daya kwaso, wanka yayi yakwanta danyin bacci, saidah kash wayar sah tafara ringing dubawa yayi yaga Aisha tela ce, daa kamar baxai dauka bah yadauka, muryantah Dan siriri tayi masa sallama ya amsa dah tashi mai kashewa Aisha jiki, yayanah kaje gida lfy, Alhamdulillah kefa, nima hakan, Kai fans in takaice muku labari haka nabarsu naja qofa nayi dakin Safia dan dauko muku labari Safia kuwa Allah Allah take gari yawaye Haneefah takuma dawowa ahaka tana tah murnan haduwar su har bacci yayi awon gaba dah ita, Bayan nabar dakin Safia neh naji kamar maganar mutum wai ashe kunsan meh, Hmmm Aisha tela ce uwar naci waya suke har yanxu, tofa ina fans dinah masu fada akan ikbar saiku dage dah sallan dare dan Aisha tela fah badama tafada cikin kogin so, haka har naji tace su hadu a WhatsApp, killer pics natah tah tura mishi amman Sam ikbar banjin komai akanta shi kawai amastayin er uwa ya dauke tah kuma bayan Safia dah mama itace mace tah farko dayake mu amala dah itah, wow aman fah kinsa nah daskare akan gado wlh kinyi kyau sosai, wai hakan dah ikbar yace bah qarramin kumburar dah kan Aisha tela yi bah jitayi kamar tah mutu dan dadi Amman sai tah maze tace "kadai fadi gaskia ai kasan banda kyau sosai fah, haba dai ai sai kisa nace niban taba ganin mace mai kyaun ki bah, Hmmm kadai fadamin gaskia, wlh Aisha dagaske fah, wanan maganan dah ikbar yayi nacewa Aisha mai kyau ce shine yasa tah canxa takun tah, hakah suka dinga chatting har sukayi sallama ikbar yah yakwanta bacci, ita kuwa Aisha baccin yaqi zuwa matah sai tunanin ikbar take tanah murnan kalmomin sah, saidah kuma kash duk yanda taso nuna masa tanasan sah dah dabara ikbar bai fahimta bah sakamakon bai taba yin soyayya bah, haka tah dinga tunani har bacci yadauke tah, Washe gari deezat tah jira Almustapha yayi matah magana amman sam shuru baiyiba hakan yasah tah dan rasa sukuni, haushin kanta tah soma jee tafara maganganu KAmar haka " Mtwss mutum dama baki sani bah harya isa yaraina miki hankali wani protection xaiban wanda kudin babana baxai bani bah, ahaka xamuyi bro n Sis din Mtwww tsaki takuma bugawa tareda fadin bullsh*t I hate guys they are disgusting, the other time wani coward yayi embarrassing dinah at the club yanxu hakan yasa dole bah canxa club bayan nagama popular awancan, tanah Cikin hakan neh taji phone natah yayi beeping alamun facebook message neh yashigo tsintar kanta dah saurin daukan phone tayi saidai kash bah Almustapha baneh Ilham ce tayi tagging dinta, haushi taji yakama tah, Hhhhh fans yanxu fah itama babban burin Ilham shine taga Almustapha tah bayyana masah yanda takamu dah love at first sight amman saidai kash haduwar su yah gagara, domin koh a club dah ita ake rufewa yanxu dan kullum tanasa hope xaixo club su hadu,
Join Us On
Twitter @BABA MONO HAXOR
Join Us On
Twitter @BABA MONO HAXOR
| Name | Telephone | Telephone |
|---|---|---|
| Haxor | +2348108811856 | +2348106384398 |
| Baba Mono Haxor | |
| Babamono_haxor |
Babamono_haxor
Google +
Baba Mono Haxor
YouTube
Baba Mono Haxor
No comments:
Post a Comment