• Mace-Guda-Daya-Tilo-Part-1-One
    Mace-Guda-Daya-Tilo-Part-1-One
  •                                         Matashin saurayine sanye da kayan yan
                                        bautar kasa (N. Y. S. C) kayan sunyi mutukar
                                       yimasa kyau, tsaye yake agaban allo yana yiwa
                                       dalibai yan department of sociology lecture din
                                         biology, a jami'ar tarayya dake jihar bauchi,

                                        kowanne dalibi ya nutsu yana sauraron lecture
                                       din domin babu karya malamin akwai iya darasi 
                                        kuma akwai zakin murya radau,wannan shine
    shigarsa hall din na 3 ,yauma kamar kullum ya
    kwashe fiyeda awa 1 yana yimusu lecture akan
    introduction to biology, kwas kwas sukaji tafiyar
    takalmi alamun ana shigowa cikin hall din,
    hankalin kowa yakoma kanta, jiyowa shima yayi
    yabita da kallo daga sama har kasa, farace
    sosai dan har yellow take dan tsabar fari, bata
    da tsayi sosai amma tana da dan jiki,
    idanuwanta manya ne farare tas,tanada dogon
    hanci da dan mitsitsin baki, tana sanye da wani
    pink din leshi da mayafinsa takalmin kafarta
    kuwa mai dan karen tsinine shima pink
    hannunta rike da jaka pink colour, kanta tsaye
    ta nufi inda zata zauna, he! Taji malamin ya
    fada ko jiyowa batayi ba taci gaba da tafiyarta.
    [3/11, 6:16 PM] Ummi A'isha: MACE GUDA
    DAYA TILO...2⃣


    Na
    UMMI A'ISHA
    Cike da haushi yabi bayanta yasha gabanta
    tare da nuna mata hanyar fita get out from my
    class taji yafada, idanuwanta ta bude sosai
    tafara kallonsa farine tas dogo mai tsananin
    kyau yana da idanuwa sosai hancinsa tamkar
    biro kuma yana da yar kiba daidai misali ita
    kanta tasan yanada kyau kuma ya hadu kallon
    banza ta wurga masa tare da Jan wani dogon
    tsaki, mamaki ne ya kamashi dan babu macen
    da ta taba yi masa tsaki sai wannan yarinyar
    yar rainin hankali, tsawa ya daka mata yace
    who are you dazaki shigo min class yanzu? Me
    kike takama dashi? Ke yar gidan uban waye?
    Gaba daya ajin yayi tsit kowa ya zuba ido yana
    kallonsu domin idan da sabo to sun gama
    sabawa da halin wannan dalibar wani mugun
    kallo ya bita dashi sannam yace oya carry your
    legs and get out from my class tun kafin na
    wulakanta ki, ni banma taba ganin wannan
    fuskar taki acikin class dina ba, ita kuwa gaba
    daya bakin cikin duniya yagama rufeta batare da
    tace masa ko kala ba tajuya tafice daga cikin
    hall din zuciyarta cike da bacin rai, lalle gayen
    nan yau xan nuna masa ko ni wacece zaisan
    dani da sauran matan da yasaba yiwa wulakanci
    akwai banbanci ayau sai naga waye ubansa a
    kasar nan.
    [3/11, 6:18 PM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILOģ

    Na
    UMMI A'ISHA
    Dawowa yayi yahau kan step din yaci gaba
    da lecture din daya keyi, Director din makarantar
    ne yashigo cikin hall din shida mukarrabansa
    nan da nan idon kowa ya koma kansu wanda
    ciki harda shi kansa malamin, dasauri director
    din yazo gabansa yana cewa me yahadaka da
    wannan yarinyar junaida mukhtar? Kasan ko
    wacece ita? Bude baki copper din yayi tareda
    niyyar yin magana amma cikin tsawa director
    din ya katse shi tare da cewa look Lamin kaifa
    ba staff dinmu bane service kawai kazo yi dan
    haka mun dakatar dakai daga wannan
    aikin,yanzu ka biyoni office inada magana dakai
    yana kaiwa nan ya juya yafita shida wadanda
    suka rakoshi, ajin kuwa tsit kakeji kamar ruwa
    yacisu shi kuwa malamin wanda aka kira da
    lamin kayansa yashiga tattarawa ya rufe laptop
    dinsa ya saka acikin jakarta ya yiwa daliban
    sallama wadanda akalla zasu kai kimanin dari
    biyu kasancewar combined lecture ne
    [3/11, 6:22 PM] Ummi A'isha: MACE GUDA
    DAYA TILO
    ģ

    Na
    UMMI A'ISHA
    Gaba daya yan ajin jikinsu yayi sanyi domin
    wannan bashine karo na farko da dalibar tayi
    sanadiyyar korar malaman makarantar ba,
    ahankali ya gama hada kayansa cikin jakar ya
    dauka ya rataya akafadarsa ya sauko ya futa
    daga cikin hall din, yana fita hall din ya cika da
    surutun daliban dake ciki, wasu tausaya masa
    suke wasu kuma bakin cikin tafiyarsa suke
    yayinda wasu kuma suke Allah wadai da halin
    wannan dalibar mai suna junaida mukhtar.
    Kansa tsaye ya nufi admin block,office din
    director ya shiga suna zaune shida students
    affairs da registerer da hed of department can
    gefe kuma wannan kyakkyawar yarinyar ce
    zaune tana kallonsa, da sallama yashiga suka
    amsa tareda nuna masa kujerar da zai zauna,
    yana zama director yafara balbale shi da fada
    tareda cewa yazama dole kabata hakuri kuma
    ka nemi afuwarta akan abinda yafaru dazu baki
    ya bude cike da mamaki wai shine zai bawa
    wannan yarinyar hakuri instead ace itace zata
    nemi afuwarshi kallo yabisu dashi daya bayan
    daya sannan yace impossible yaza ayi ace nine
    zan bata hakuri bayan itace tayi min laifi? Head
    of department ne ya katse shi ta hanyar cewa
    kasan yar gidan waye kuwa? Ko yar gidan waye
    wlhi bazan bata hakuri ba kallonsa suka farayi
    cike da mamaki director yace to ai kuwa tunda
    bazaka bata hakuri ba yazama dole kabar
    makarantar nan ayau.
    [3/11, 6:23 PM] Ummi A'isha: MACE GUDA
    DAYA TILO
    ģ

    Na
    UMMI A'ISHA
    Mamakine karara ya bayyana akan fuskarsa
    domin kuwa babu dalilin da zaisa akoreshi akan
    kawai ya hukunta dalibarsa wacce ta karya
    dokarsa, wata xungureriyar takarda director ya
    miko masa yace gashi ka zaba acikin biyu
    nafarko ko kabawa junaida hakuri ko kuma ayau
    dinnan ka bar mana makarantar nan domin
    bazamu zuba maka ido ka yimana sanadin
    aikinmu ba, wannan yarinyar babanta shine
    permanent secretary na education kuma shine
    Head of service na wannan state din dan haka
    kazabi daya, shiru lamin yayi yana tunani wato
    dan babanta ne head of service shikenan sai ta
    raina mutane? Shi ai ya zata duk wannan
    kafafar da take babanta ne governor dama head
    of service ne kawai? Wani guntun tsaki yaja
    aransa yace lallai nima dan bakusan waye ni ba
    shiyasa kuke neman wulakanta ni,ni ai ubana
    yafi nata matsayi tunda secretary to the state
    government ne kaf state dinmu ubana shine na
    3 daga governor sai deputy sai ubana amma
    ban taba nunawa ba registerer ne ya katse masa
    tunani ta hanyar cewa lamin kaifa muke jira kayi
    magana kallonsu yayi sannan ya juya ya kalli
    yarinyar yace wlhi bata isa nabata hakuri ba
    nazabi barin makarantar, takardar ya karba ya
    tashi yafita daga cikin office din ya nufi motarsa
    wadda ke ajiye awurin da aka tanada domin
    ajiye motoci.
    [3/22, 7:56 PM] Ummi A'isha🏻: [3/15, 7:05 AM]
    Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO
    ģ

    Na
    UMMI A'ISHA
    Motarsa kirar Toyota corolla yabude ya shiga
    ya fita daga cikin makarantar ,gudu yake
    shararawa sosai kamar wadda zai tashi sama
    yafita daga garin bauchi ya nufi birnin yola.
    Karfe 3 dai dai yashiga cikin yola Chief olusegun
    obasanjo housing estate ya nufa, ahankali yake
    tukin har ya iso tangamemen gidan nasu wanda
    yake cikin jerin gwanon gidajen, hon yayi mai
    gadi ya bude masa gate din yashiga cikin gidan
    securities sai daga masa hannu suke yi ajiye
    motar yayi a muhallinsa sannan ya tasamma
    cikin gidan, babban falon gidan ya shiga daya
    daga cikin kannenshi ya hango kwance cikin
    luntsumemiyar kujera tana kallon Indian film
    sallama yayi dasauri ta dago tana cewa oyoyo
    yaya lamin karasowa ciki yayi yana cewa
    wacece? Hasna ce ko husna? Murmushi itama
    tayi tace yaya kenan wai kai meyasa baka
    ganemu? Dariya yayi mata sannan yace to
    mummy da daddy ma basa ganeku balle ni da
    bani na haifeku ba dariyar itama tayi sannan
    tace to husna ce hasna na kitchen tana yimana
    fried indomie murmushi yayi yace sarakan
    kwadayi kenan ina mummy? Mummy tana side
    din dad tabashi amsa mikewa yayi ya nufi side
    dinshi.
    [3/15, 7:08 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILOģ

    Na UMMI A'ISHA
    Dakinsa yashiga ya zauna ya zubawa carpet
    din dake malale acikin dakin ido, tunanin
    matakin da zai dauka akan wannan yarinyar shin
    me take takama dashi? Yanzu kenan duk burin
    da ya dauka ya rushe? Babban burinsa shine
    yayi lecturing lokacin service dinsa domin yana
    kaunar koyarwa a jami'a amma yau gashi wata
    MACE GUDA DAYA TILo tayi masa sanadi ta
    rusa masa duk budget dinsa ai kuwa yazama
    tilas ya rama wannan wulakancin da tayi masa
    da wannan shawara ya tashi ya shiga hadadden
    toilet dinsa yayi wanka ya fito yashirya cikin
    wata green din t shirt mai hoton heart ajiki sai
    blue din jeans ya taje sumar kansa ya fesa
    turaren smart collection ya fito, falon
    mummynsa ya wuce yana shiga ya tarar da ita
    zaune cikin kawatacciyar shiga tana waya
    gefenta yan biyunta ne zqune suna cin
    indomie,kusa dasu yaje yazauna yana fadin
    hasna kin gama girkin dasauri kanwar tasa ta
    kalleshi tana fadin lah yaya lamin yaushe ka
    dawo? Ban jima da dawowa ba ya bata amsa
    dai dai lokacin mummyn tasu ta gama wayar ta
    kalleshi tana cewa babana saukar yaushe? Wlh
    dazu nadawo mummy daddy yana gari kuwa?
    Kallonsa tayi tace bakuyi waya bane? Dazun nan
    yadawo daga Holland kaje ka sameshi yana falo
    mikewa yayi ya nufi falon mahaifin nasa.
    [3/15, 7:12 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILOģ

    Na UMMI A'ISHA
    Ahankali yake ratsa falikan har ya isa na
    mahaifin nasa ya sameshi zaune yana hutawa
    sallama yayi masa sannan ya nemi wuri ya
    zauna yafara gaida shi cikin murmushi mahaifin
    nasa ya amsa sannan yace lamin har kadawo
    daga bauchin? Jikinsa asanyaye yace dady sun
    sallameni sunce sai dai naje wani wurin nayi
    service din kallonsa mahaifin nasa yayi sannan
    yace laifin me kayi musu? Kansa ya sunkuyar
    kasa sannan yace babu laifin komai daddy to
    yanzu ya zakayi? Ya tambayeshi dama daddy
    cewa nayi yanzu zan koma can N. Y. S. C
    Secretariat din na sanar musu inyaso sai ayi
    posting dina Bayero university kano ina ganin
    hakan zaifi, to shikenan Allah yasa hakan shi
    yafi alkhairi mahaifin nasa yace dashi amin ya
    amsa sannan yatashi ya fita daga cikin falon.
    Ita kuwa junaida tana tashi daga office din
    director tashiga sabuwar motarta kia 1 door ta
    nufi gidansu dake unguwar area 7 tana isa ta
    wuce dakinta ta jefar da jakarta, mayafinta,
    takalminta, wayarta ta haye gadonta ta kwanta
    rufe idonta keda wuya tafara ganin wannan
    saurayin matashin yana yimata gizo gaskiya
    babu karya ya hadu zuciyarta taji tafara dukan
    uku uku kamar zata tsage, idanuwanta ta bude
    sannan ta mayar ta rufe still shi din dai take
    gani lokacin da yake yayyafa mata masifa acikin
    hall din.
    [3/15, 7:13 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILOģ

    Na UMMI A'ISHA
    Zaune ta tashi cikin sauri, Fara zagaya cikin
    dakin nata tayi sannan ta saki wani kayataccen
    murmushi toilet ta shiga ta silla wanka sannan
    ta fito ta sanya wata doguwar riga ta shan iska
    ta nufi falo acan ta hango mahaifiyarta zaune
    tana kallo karasawa tayi cike da shagwaba ta
    fada kan cinyarta tana cewa umma nifa yunwa
    nake ji dasauri takalleta tace haba autana me
    yasa kike son zama da yunwa kira tafara
    kwallawa daya daga cikin yan aikin gidan
    dagudu ta runtumo tazo ta durkusa agabansu
    kallon junada ta yi tace auta me zaki ci?? A
    yangance tace ta dafa min indomie with egg da
    sauri mai aikin ta tashi ta nufi kitchen domin
    aiwatar da abinda aka sata ita kuma taci gaba
    da zubawa uwar shagwaba.
    [3/15, 7:15 AM] Ummi A'isha: MACE GUDA
    DAYA TILO..
    ƒ£0⃣

    Na UMMI A'ISHA
    Tun da sassafe lamin ya baro garin Adamawa
    ya nufi bauchi gudu yake babu kakkautawa ya
    kure A. C din motar ya kunna wakar no one be
    like you yana saurare amma acan kasan ransa
    kuwa abinda zai aiwatar kawai yake tunani.
    Karfe takwas ya shiga cikin bauchi dan haka
    wani guest house ya zarce inda zai huta. Sai 10
    ya fito yashiga cikin garin kofar jami'ar yaje ya
    yi packing yana ganin shige da ficen daliban
    yana nan xaune acikin motarsa ya rurrufe glass
    din wanda ya kasance mai mutukar duhu ne na
    waje baya ganin na ciki sai na cikine ke hango
    na waje, wata mota pink colour ya hango tana
    tahowa kirar new discussion R888 sai datazo
    saitinsa sannan yaga ashe wannan yarinyarce
    junada aciki tasha ado tamkar wata sarauniya
    komai blue nan da nan ta kutsa kan motar tata
    cikin makarantar shi kuwa murmushin mugunta
    yayi tareda fadin yarinya kin tabo gidan rina dan
    haka zaki yi bayani.
    [3/22, 7:56 PM] Ummi A'isha🏻: [3/17, 9:52 AM]
    Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO..
    ƒ£1⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Yana nan zaune har ya hango adam dama
    shi yake jira, Adam daya daga cikin dalibansa ne
    wanda yafara koya musu kuma course mate din
    junada mukhtar ne shigowa motar adam din
    yayi sannan yafara gaida lamin ta hanyar cewa
    morning sir, morning lamin din ya amsa yace
    dama zuwa nayi kabani duk labarin da kasani
    akan wannan yarinyar junada mukhtar murmushi
    Adam yayi sannan yafara bashi labarin. Alhaji
    mukhtar Magashi shine mahaifinta kuma
    asalinsu yan garin bauchi ne cikin karamar
    hukumar Giyade babanta ya rike madafan iko da
    yawa daga karshe aka bashi mikamin head of
    service na wannan jahar matarsa 1 da yaransu
    uku junada ce yar auta sai yayunta maza guda 2
    Khalid da Amir, yar gatace ta karshe kasancewar
    ita kadai ce mace kuma gata yar auta komai
    daka sani na rayuwa yimata ake bata da wata
    matsala sai kwaya daya.
    [3/17, 9:54 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO...ƒ£2⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Matsalarta shine bata son karatu ko kadan
    gata shagwababbiya ce ta karshe amma duk da
    haka mahaifinta yana hukuntata idan ta aikata
    ba dai dai ba sai dai ita mahaifiyarta tafi batata
    don bata tsawatar mata idan tayi ba dai ba,
    tunda muka shigo makarantar nan bata zuwa
    lecture sai time din data gadama, bata
    respecting din malamai balle yan uwanta dalibai
    bata da lokacin tsayawa tayi karatu amma kuma
    babu malamin da ya isa yabata carry over
    saboda director yana daure mata gindi, yana iya
    korar mutum akanta saboda kawai yana jin
    tsoron kar ta fadawa mahaifinta abashi query
    bayan kuma shi mahaifinta ba irin wadannan
    mutanen bane masu zarmewa akan yayansu, ka
    ganta nan har muka shiga level 300 bata taba
    samun carry over ba alhalin kuma ba karatun
    takeyi ba. Wani matashin murmushi lamin yayi
    tabbas yanzu ya samu hanyar da zai rama
    abunda tayi masa ta hanya mai sauki juyawa
    yayi ga Adam yayi masa godiya sannan ya yi
    masa sallama yatashi motarsa ya bar wurin,
    garin kano ya nufa yana tafe yana nishadi ya
    kunna wakar you are my African queen ahaka
    har ya isa B. U. K.
    [3/17, 9:56 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO..ƒ£3⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Yana isa ya kai takardunsa cikin sa'a sukayi
    accepting dinsa musamman ma da suka ga
    cewar ba a Nigeria yayi karatunsa ba a Malaysia
    yake yi, psychology department suka turashi
    suka bashi yan level 100 inda zai daukesu
    Biology, sati 1 suka bashi tareda bashi inda zai
    zauna amma bai karbi masaukin ba kasancewar
    yanada inda zai zauna. Karfe 4 yagama abinda
    zaiyi yabar cikin makarantar ya nufi yola. Bai
    isa garin yola ba sai kimanin karfe 7 nadare
    yana zuwa mahaifinsa ma na karasowa dan
    haka cikin gidan ya shiga yajira karasowar
    mahaifin nashi wanda bodyguard dinsa suka
    ysnyameshi kamar wanda za adauke,da
    fara'arsa ya tari dan nasa yana fadin tafiya tayi
    sauri my son dafatan andace? Murmushi yayi
    sannan yace yes dad sunyi accepting dina dafa
    kafadarsa uban yayi tareda jan hannunsa suka
    jera suna tafiya tamkar wasu abokai har suka
    karasa cikin falon uban sannan shi lamin din ya
    juya ya wuce side din mummy yana shiga ya
    tarar da babban yayansa yana zaune yana cin
    abinci akan dinning wajensa yakarasa yabashi
    hannu suka gaisa sannan shima ya nemi wuri ya
    zauna yace broz nabar bauchi university fa na
    koma kano murmushi yayan nasa yayi wanda
    suke mutukar kama amma shi bakine sabanin
    lamin wanda yake fari sol, dubansa yayi yace to
    nidai ina baka shawara wlhi babu kai babu yan
    matan jami'a, dan nasan halinka da shegen
    neman mata.
    [3/17, 9:59 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO...ƒ£4⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Kai ko tsoron Allah bakaji balle tsoron
    wadannan cutukan na zamani, rai lamin yabata
    sannan yace kaifa kanada takurawa wlh
    shigowar mahaifiyarsu ne yasashi yin shiru
    domin baya son taji zancen da yakeyi
    kasancewar yanada yakinin duk gidan babu
    wanda yasan yana neman mata in banda yayan
    nasa cikeda murna tace sannu babana shima
    cikin sigar shagwaba yace yawwa mummy dama
    nazo miki da wani albishir murmushi tayi tace to
    Allah yasa alkhairi ne ai kuwa mummy alkhairi
    ne kuma nasan zakiyi farin ciki sosai kallonsa
    suka tsaya yi itada yayan nasa tace to fadi inji
    cikin farin ciki yace na samo matar aure a
    bauchi dan haka kisanar da dad aje a tambayo
    min domin aure nake so, wani farin cikine ya
    lullube uwar tace to Allah yasa albarka kuma
    naji dadi bayan kagama karatu za ayi bikin?
    Dasauri yace no nanda 3 months nake so ayi
    cikin mamaki tace to zai yiwu ahada da na
    abdulrahman yayankane? Yes mum haka nake
    so ayi cikin fara'a tace to Allah ya yarda tatashi
    ta fita daga cikin falon. Yayansa ne ya kalleshi
    yace ai gara kayi auren yafi maka amma kana
    yaronka dakai sai jarabar mata just 26 years?
    Koni da nake 29 bana bin mata sai kai? Cikin
    kunkuni lamin ya mike yabar cikin falon ya nufi
    side dinshi aransa kuwa fadi yake wannan
    dinma da zanyi ai na ramuwar gayya zanyi bana
    Allah bane.
    [3/17, 10:00 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO...ƒ£5⃣

    Na UMMI A'ISHA
    Yana shiga hadaden dakinsa wanda ya
    kawatu mutuka da kayan alatun more rayuwa ya
    fada saman gado ya jawo wayarsa BlackBerry
    B210 Vicky yakira daya daga cikin yanmatansa
    ringing 2 ta dauka cikin harshen turanci tafara
    gaida shi murmushi yayi yace nayi missing dinki
    daga can kamar zatayi kuka tace nafika damuwa
    da rashinka kusa dani yanzu yaushe zakazo?
    Silin din dakin ya kurawa ido yace gaskiya Vicky
    zaki dade baki ganni ba amma next week zan
    shigo kano to idan nazo i will call you murmushi
    tayi tace ok sai najika i luv you, luv you too ya
    amsa mata ya ajiye wayar ko minti 2 ba ayiba
    wayar tasa tasoma ruri hannu ya mika ya dauko
    yana dubawa yaga Jenifer ce cikin murmushi
    yaje hello madam j how are you? Daga can ta
    amsa da fine my Prince.
    [3/22, 7:56 PM] Ummi A'isha🏻: [3/22, 4:21 PM]
    Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO..
    ƒ£6⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Kamar zata saka kuka tace yaushe zamu
    hadu? Wani malalacin murmushi yayi sannan
    yace very soon but yanzu ina yola ne kin san
    babu halin kizo amma idan nasamu time zanzo
    dakaina cike da jin dadi tace to ina jiranka i love
    you me too yabata amsa ya kife wayar. Daya
    wayar tashi ce ta soma kara ya dauka ya duba
    sunan Mary yaga ajikin screen din cikin sauri ya
    daga yace hello my Mary yakike? Daga can tace
    abnormal murmushi ya aika mata dashi yace
    what's wrong? Cikin shesshekar kuka tace
    kamanta dani kwana biyu baka nemana
    rarrashinta yafara yi domin duk cikin yanmatan
    sa itace star yafi ji da ita domin Mary akwai
    kyau ga diri shiyasa ma yafi sonta fiyeda sauran
    dakyar ya samu ya lallasheta tadaina kukan
    sannan yayi mata alqawarin zai tura mata kudi
    ta account dinta sai ta yanki ticket din jirgi daga
    Lagos tazo kano ta sameshi saida yayi da gaske
    sannan ta hakura sukayi sallama yana ajiye
    wayar yaga yayansa daga bakin kofa yana tsaye
    yana kallonsa fuskarsa babu walwala yace lamin
    abinda kakeyi baka kyautawa wai kai me yayan
    arnan nan suke baka ne ka manne musu? Wlh
    kaji tsoron Allah dan babu mamaki yanzu yana
    fushi dakai kuma inajin ma har giya kana sha
    sai asannan lamin yayi magana yace ni babu
    abinda nake sha nasan dai ina neman mata
    amma bana shan ko sigari balle giya.
    [3/22, 4:22 PM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO...ƒ£7⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Harara ya wurga masa sannan yace kalli lips
    dinka yadda sukayi ja ahaka xakace min baka
    shan giya na yarda? Kallonsa yayi yace yaya sai
    dai idan sharri zaka yimin amma wlh bana shan
    giya hararsa ya kuma yi yace kaji dashi dai ya
    juya yayi ficewarsa shi kuwa lamin tashi yayi ya
    shiga toilet domin watsa ruwa. Abangaren
    junada kuwa tun ranar data sa aka kori lamin
    duniya tayi mata zafi domin ta tsinci kanta
    dumu dumu cikin kaunarsa gashi bata san a
    inda yake ba bare tasa anemo mata shi, yauma
    ranta abace ta shirya cikin wani brown din
    material ta nufi sch amma sam zuciyarta babu
    dadi gaba daya ranta abace yake kuma ko yaya
    ta rufe idanuwanta shi take gani abinda yafi
    tsaya mata arai shine yadda kullum sai tayi
    mafarkin kyakkyawar fuskarshi, ranta ajagule ta
    fito daga dakinta ko ummarta bata yiwa sallama
    ba ta fita sabuwar motarta Prado baka ta dauka
    ta nufi makarantar zuciyarta cike da fatan dama
    taga wannan matashin saurayin.
    [3/22, 4:24 PM] Ummi A'isha: MACE GUDA
    DAYA TILO...
    ƒ£8⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Da wannan tunanin ta isa cikin makaranta kowa
    mamakin canjawarta yake tun ranar da abin
    yafaru bata kara yiwa kowa maganar bacin rai
    ba sannan yanzu ta daina makara da wuri take
    zuwa school sabanin da dasai lokacin data
    gadama kuma babu wanda ya isa ya hanata
    shiga lecture, ahankali tashiga hall din ta zauna
    ziciyarta cike da dana sanin fadawa director
    datayi har aka kori wannan dan bautar kasar da
    haka tagama sauraron lectures din ta tashi ta
    tafi gida. Shi kuwa lamin tuni yafara zuwa
    lecturing a kano B. U. K wani dan madaidaicin
    gida ya kama a unguwar jan bulo kabuga tuni
    budurwarsa Vicky ta yi masauki agidan tana
    tafiya Mary tazo, haka ya rinka sheke ayarsa
    batare da iyayensa sun sani ba dama ko lokacin
    da yake Malaysia haka haka yake ajiyesu
    agidansa daga wannan ta tafi wannan zatazo.
    Yan matan jami'a kuwa ba acewa komai domin
    ganinshi kyakkyawa mai class kuma ga kudi nan
    da nan suka Fara cusa kansu wurinsa sai dai
    har yanzu babu wadda ta samu shiga domin shi
    baya harka da hausawa duk yan matansa
    Christian ne babu musulma ko daya kuma
    bashida standard budurwa domin bai shirya aure
    yanzu ba sai auren ramuwar gayya.
    [3/22, 4:25 PM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO...ƒ£9⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Yau tunda yagama lecture yakoma gida yafara
    hada kayansa ya gama Mary dake kwance tana
    bacci yafara tashi dakyar ta tashi tana faman
    murtsuke ido tana tambayarsa har yadawo eh
    ya amsa mata sannan yace kitashi ki shirya
    kitafi sai next week zan dawo kinga yanzu ni
    nagama shiryawa kamar mai shirin yin kuka tace
    to sai munyi waya tashi yayi yadau jakarsa
    yatafi tareda bar mata sallahun idan tagama ta
    rufe gidan. Karfe 2 na rana ya isa gida mummy
    yatarar zaune afalo yan biyunta sun zagayeta
    sai surutu suke mata ganinsa da sukayi yasa
    suka dan nutsu suna fadin oyoyo yaya harara
    yabisu da ita yace kunzo kun wani zagayeta
    kamar wasu kananan yara, ke hasna kin share
    min dakin dana saki? Dasauri tace yaya bani
    bace sai dai ko husna cikin sauri itama tace wlh
    bani bace banza yayi dasu domin dama haka
    suke masa irin wannan rainin hankalin idan yasa
    daya aiki to idan batayi ba sun rika cewa wance
    ce itama dayar tace ba ita bace ,mummy ya
    kalla yace mummy ina wuni cikin fara'a tace lfy
    babana kallonta ya sakeyi yace yakukayi da
    dady akan maganar nan? Dariya tayi tace kaifa
    kafiya zumudi ai mun gama maganar dashi
    ashema yar gidan Alh mukhtar magashi ce? Ai
    tuni dadynku yayi masa magana kuma yace bai
    mata miji ba dan haka yabaka ita yanzu saura
    aje ayanke rana, farin ciki ne ya cikashi ya mike
    ya nufi side dinshi.
    [3/22, 4:27 PM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO..ƒ£0⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Zuciyarsa fes ya shiga dakinsa yasamu wuri
    ya zauna yana tunanin ta inda zai bullowa
    wannan yarinyar junada. Mukhtar wani
    malalacin murmushi yayi dalilin samo abinda
    zaiyi mata cikin haka yaji phone dinshi tana kara
    ahankali ya cirota daga cikin wandon jeans din
    dake jikinsa Angelina yagani a rubuce tsaki yayi
    ya ajiye wayar batare da ya daga ba daga
    karshema da yaga tana neman damunshi sai ya
    kashe wayar gaba daya. Ita kuwa junada kullum
    da tunanin lamin take kwana take tashi kafin ta
    ankara sonsa yagama cika zuciyarta, yau kamar
    kullum ta dawo daga school ta kwanta tayi
    bacci ta huta sannan tayi wanka ta fita zuwa
    falo amma bataga mahaifiyarta ba dan haka ta
    wuce dakinta adakin ta sameta tana zaune
    bakin gado tana waya kusada ita taje ta zauna
    tana sauraronta har tagama, gamawarta keda
    wuya ta juyo gareta tana cewa junada har kin
    tashi daga barcin? Dazu nashiga dakin naki
    naga kina bacci dama mahaifinki ne yabani sako
    nasanar dake yabada ke ga dan abokinsa ras
    junada taji gabanta yafadi kallon mahaifiyar tata
    tayi sannan tace a ina yake? Murmushi uwar
    tayi sannan tace dan gidan Alh kabir sulaiman
    yola ne mahaifinshi shine SSG na Adamawa
    state kuma yanada sarauta makaman Adamawa
    Turakin yola gashi kuma classmate din
    mahaifinki ne domin tare sukayi makaranta
    kedai kawai abinda nake so dake shine kiyi
    kokari kiyi biyayya insha Allahu zakiji dadi agaba
    don kin san mahaifinki bazai taba zaba miki
    mijin da ba nagari ba ita dai junada shiru tayi
    batace komai ba domin hankalinta yagama tashi
    amma duk da haka ta kuduri niyyar yiwa
    mahaifinta biyayya ahankali tace to umma naji
    abinda kikace Allah ya zaba min mafi alkhairi
    cikin jin dadi mahaiyarta tace amin Allah yayi
    miki albarka.
    [3/22, 7:56 PM] Ummi A'isha: [3/22, 4:37 PM]
    Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO...
    ƒ£1⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Tuni mahaifin lamin ya shirya shida yan
    tawagarsa yaje gidan su junada domin nemawa
    dansa aurenta batareda wani bata lokaciba
    mahaifinta ya amince tareda sanya ranar auren
    dai dai da ranar da za ayi na yayansa
    Abdulrahman sun rabu cike da farin ciki da
    girmama juna, ita dai junada bata cewa domin
    dama bata damu da tasan ko waye angon ba
    saboda tasan ba zabinta bane zabin iyaye ne
    (sunan wani littafi na hafsata bounzer) dan haka
    kawai hidimar gabanta takeyi. Abangaren lamin
    kuwa yafi kowa murna da sanya wannan rana,
    tuni ya koma kano yaje ya dora daga inda ya
    tsaya wannan karon Angelina da blessing ne
    suka je gidan nasa amma kullum cikin fada suke
    da zarar ya fita zasu fara dambe ganin haka
    yasa ya tattarasu yakora yayiwa Mary waya
    yace tazo.
    [3/22, 4:39 PM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO...ƒ£2⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Biki ya rage saura sati 2 lamin ya shirya
    shida yayansa sukaje bauchi domin gaisheda
    iyayen junada ita kuwa lokacin bama ta kasar
    sun tafi sudan itada kanwar mahaifiyarta mami
    inda za ayi mata gyaran jiki da sauran abubuwa
    na amare kuma bazasu dawo ba sai ana saura 3
    days biki,cike da girmamawa da mutuntawa su
    lamin suka gaisa da kowa lfy sannan suka koma
    yola inda acanma shirye shiryen bikin ake tayi
    dan har an harhada lefe aranar aka kai na matar
    abdulrahman mai suna kausar yar gidan sarkin
    yola ce yayinda na junada akace sai washe gari.
    Hakan kuwa akayi washe gari yan kaiwa kaya
    suka nufi bauchi kayane na kece raini akwati 24
    set daya brown daya set din kuma pink colour
    yan uwan junada sunyi mutukar murna hakan
    nema yasa suka bada tukwici na naira dubu dari
    biyu. Tunda biki ya rage saura kwana 8 gidansu
    lamin suka fara shirye shiryen komawa sabon
    gida domin acanne za a gudanar da bikin, wani
    tangamemen gida state government ta ginawa
    mahaifinsu akusada government house gidan
    unguwa gudane domin part guda 5 ne acikin
    gidan dan haka ananma su lamin din zasu
    zauna.
    [3/22, 4:40 PM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO..ƒ£3⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Ana saura kwana 3 biki su junada suka dawo
    daga Sudan tasha gyara tayi tsananin kyau sai
    sheki da kyalli take tamkar wata tauraruwa,
    gaba daya ta yi wata kala ga uwar rama datayi
    saboda bata iya cin abinci. Shi kuwa lamin
    baima yi gayya ba domin acewarsa wannan ba
    biki zaiyi ba zaiyi bikinsa sai nan gaba yanzu
    bai isa aureba, ana igobe za afara shagalin biki
    suka koma sabon gidansu anan aka fara
    gudanar da biki washe gari akaje aka daura
    auren Abdulrahman da Kausar sannan aka wuce
    garin bauchi inda jama'a sukayi dafifi domin
    jiran daurin auren, ango yayi kyau cikin wata
    shudiyar shadda wadda tasha dinki mai tsadar
    gaske 12 dai dai aka daura auren junada
    mukhtar da angonta Lamin Kabir sulaiman akan
    sadaki dubu dari, ana daura auren lamin yayi
    tafiyarsa batare da ya nemi ganin amaryar ba.
    Ita kuwa dama ko sha'awar ganin fuskarsa
    batayi domin batasan waye ba kuma bata son
    tasanshi haka aka wuni ana kade kade da raye
    raye gamida bushe bushe yamma tanayi aka
    dauki amarya sai garin yola inda aka kaita
    dakinta.
    [3/22, 4:42 PM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO..ƒ£4⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Wurin iyayen mijinta aka fara kaita sannan
    aka nufi sashenta da ita. Bayan kowa ya tafi ne
    husna da hasna suka shigo dakin nata idonta
    jajur kamar barkono tafara kallonsu dam taji
    gabanta yafadi domin sunyi mutukar yi mata
    kama da wannan copper din zama sukayi akusa
    da ita suka fara zuba mata surutu kallo ita dai
    take binsu dashi acikin ranta tana fadin waw
    identical twins dan hatta muryarsu iri dayace
    komai nasu iri daya babu ta inda suka banbanta,
    basu suka bar side dinta ba sai 10 nadare ita
    kuwa zaune tayi tana ta faman kuka shiru shiru
    babu ango babu dalilinsa har bacci ya dauketa.
    Karfe 6 ta tashi tashiga tayi wanka ta shirya
    cikin wata atamfa super purple colour dinkin
    bubu yayi mutukar amsarta, window din dakinta
    ta leka girman fadin tsakar gidan ne yaso
    tsoratata don babbane sosai part biyar tagani
    duk iri daya daga can gaba katon filin wasa ne
    an sassaka kayan motsa jiki ga wurin basketball
    da volleyball nan daga gaba kuma wurin table
    tannins ne komai dai na wasa an tanada awurin
    window din tasaki takoma na daya bangaren ta
    daga wani katon swimming poll ta hango gaba
    dashi kuma garden ne kawatacce.
    [3/22, 4:44 PM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILOƒ£5⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Dakin nata tabi da kallo yasha furnitures
    masu tsada komai red da ratsin baki fitowa
    daga cikin dakin tayi wani dakin tagani yana
    kallon nata tsakiyarsu kuma dan karamin falo ne
    shima tunda ga kujerun zuwa labulayen duk red
    and black ne ga madaidaiciyar plasma tv manne
    ajikin bango, dakin dayake kallon nata ta bude
    tashiga shima babu laifi ya kawatu mutuka da
    kaya irin na zamani komai naciki red colour ne
    da toilet aciki fitowa daga ciki tayi ta murda
    kofar falon wani tangamemen falo tagani wanda
    ya sha luntsuma luntsuman kujeru har kala biyu
    daya ash colour dayan kuma pink colour ne dan
    haka labulayen ma sai suka kasance pink da
    ash colour ga wata jibgegiyar plasma manne
    abangon falon daga gaba kadan dining area ne
    taciki ga kitchen nan da store agefe, gefenta ta
    kalla shima dai wata kofar ce da alama shima
    irin dakunanta ne da dan falo aciki ma'ana dai
    sun saka tangamemen falon a tsakiya sukuma
    suna facing din juna dan haka shima ji tayi tana
    sha'awar ganin yanda aka tsarashi da karfin
    gwiwarta ta murda kofar tashiga dan karamin
    falo ne kamar nata da kujeru light green kanta
    ta daga tafara bin hotunan dake manne ajikin
    bangon falon da kallo cak! Taji numfashinta ya
    tsaya sakamakon ganinsa da tayi ajikin
    tangamemen hoton yana sanye da bakar riga ya
    gyara sumarsa yana murmushi.
    [3/23, 9:51 AM] Ummi A'isha🏻: [3/23, 9:21 AM]
    Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO
    ƒ£6⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Idanuwansa manya farare tatas kamar an
    diga zaiba aciki babu abinda yafi burgeta irin
    jajayen lips dinsa yayi bala'in yimata kyau sosai
    dadine ya kamata azuciyarta tafara fadin ya
    Allah kasa ba gizo wannan bawan naka yake
    min ba Allah kasa dagaske shine abokin
    rayuwata na har abada,sallamar da ta jiyo a
    babban falone yasata saurin fita daga cikin falon
    nasa hasna da husna tagani dauke da kayan
    breakfast sunsha ado sosai dasauri ta taresu
    tana fara'a a'a yan biyune sukazo sannunku da
    zuwa hasna ce tace sannu matar yaya ranta fari
    tas tazauna dasu suka fara hira har azahar tayi
    sannan suka bar side din nata suka koma nasu
    shiru shiru bata ga ango ba da haka har akayi
    kwana 5 da bikinsu sai dai kullum su hasna
    nazuwa su tayata hira wuni sukeyi awurinta
    wani lokacinma har dare suke kaiwa, yau tunda
    safe tafito babban falon ta zauna sallamar wata
    yar kyakkyawar mace taji ta amsa mata tashigo
    ciki bayan sun gaisa tace mata Kausar ce matar
    Abdul brother din lamin murmushi tayi tace
    sannu da zuwa yau kin fito kenan itama
    murmushin tayi tace eh yanzuma sallama nazo
    miki zamu tafi Uganda ne nida shi shiyasa nace
    baxan tafiba sai nashigo munga juna mikewa
    tayi tace yana waje yana jirana dan har mun fito
    itama mikewar tayi tabi bayanta tana cewa Allah
    ya saukeku lfy.
    MACE GUDA DAYA👆TILO
    2⃣7⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Suna fita tsakar gida ta hangoshi gabanta
    yayi mummunar faduwa ahaka suka karasa inda
    suke tsaye suna jiransu sai da sukaje daf dasu
    sannan taga ashe ba mijinta bane sai dai suna
    mutukar kama sosai amma mijinta yafishi kyau
    nesa ba kusa ba kuma yafishi fari russunawa
    tayi ta gaida shi cikin sakin fuska ya amsa su
    husna ne suka runtumo suka zo suka rungumeta
    suna dariya itama dariyar tafara yi musu
    sallama sukayi dasu Kausar suka tafi ita kuma
    su hasna tabi side din mummy yaune karo na
    farko da ta fito tun zuwanta gidan side din
    mummy irin nata ne sak,adaki ta taradda ita ta
    sunkuya har kasa ta gaida ta amsa cikin kulawa
    sannan tace ai mijin naki yace gobe zai dawo
    daga kanon ko? Dam tayi sannan tace ehh dan
    bata son mummy ta fahinci har yau bata ganshi
    ba mummyn ce taci gaba da cewa jiya nake
    cewa aturo miki masu aiki guda uku da mai
    shara da wanke wanke da mai girki sai mai
    wanki shine lamin yace ai kince baki bukata zaki
    nayi duk da kanki kuma bakida ra'ayinsu
    shiyasa ma bakiyi magana ba kanta ta daga
    tace eh ninace kar akawo itadai mummy
    mamakine ya cikata saboda daga ganin wannan
    yarinyar kasan yar hutuce babu wahala atare da
    ita amma tunda ita tace bata ra'ayi shikenan
    mikewa tayi ta shiga dakin su husna nanfa suka
    fara hira babu laifi ta saba dasu dan haka ta
    sake dasu sosai fiyeda mummy domin tana dan
    jin nauyinta anan ta wuni har yamma sai da
    la'asar lis sannan suka dunguma suka koma
    bangarenta sai wurin goma sukayi mata sallama
    suka tafi.
    MACE GUDA DAYA TILO
    ƒ£8⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Yau a lissafinta kwanasu 10 da aure amma
    bata taba dora idonta akan mijinta ba kullum ita
    take yin aikinta shara wanke wanke girkine ake
    kawo mata daga wurin mummy kullum acan
    take wuni sai dare take dawowa side dinta.
    Wanka tayi taci kwalliya cikin wani material ja
    tafito da niyyar taje wurin mummy tana fitowa
    ta hango wata sabuwar mota blue kirar
    Mercedes 2015 new model tana shigowa tana
    karasowa ciki akaje akayi packing dinta a
    garage ya bude ya fito yana sanye cikin bakar
    riga an zana stars guda uku ajiki an rubuta just
    bring it ajiki yasa bakin wando yayi mutukar
    kyau fuska adaure ya karaso inda take yace ina
    zaki? Wata irin faduwa taji gabanta yayi yayin
    da zuciyarta ke dukan uku uku ba kakkautawa
    wurin mummy zani to muje ciki ina son magana
    dake yafada yana ta faman huci sim sim ta
    wuce yana biye da ita har cikin babban falon
    kujera ya samu ya zauna yayinda ita kuma ta
    zauna can nesa dashi kallo yabita dashi sannan
    yace ke! Karkiyi tunanin ko na aureki ne dan kin
    burgeni ko dan ina sonki no na aureki ne domin
    na wulakanta ki na nuna miki ke ba kowa bace
    face baiwa dan awurina baki da maraba da
    kuyanga zan maida ke tamkar baiwa wadda
    zata zama abin kwatance agari nine nan na
    hana mummy ta kawo miki yan aiki saboda
    wannan yana daya daga cikin horon da zanyi
    miki acikin gidan nan saina gama azabtar dake
    sannan zanyi miki saki uku kwarara yanda zaki
    dade kina jin bakin ciki arayuwarki, daga yau
    kece zaki nayin duk wani aiki nawa kama daga
    abinci wankin kayana gyaran dakina da sauran
    ayyuka kuma wlh koda wasa kika fadawa
    mummy saina raunata ki banza kawai ki kalleni
    da kyau ni ba class dinki bane wlh level dina ya
    wuce naki.
    [3/23, 9:25 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILOƒ£9⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Tunda yafara bayaninsa binsa kawai take da
    ido batare da tayi koda motsi ba har ya diga aya
    wani mugun kallo ya watsa mata yace kalleta
    kamar mutuniyar kirki mai kamada aljana kawai
    sannan magana ta karshe duk abinda kika gani
    adakina kar ki kuskura ki taba mun ki bar min a
    mazauninsa idan kuma ba hakaba zaki yabawa
    aya zakinta dan sai jikinki ya gaya miki wlh
    yana kaiwa nan ya mike ya shige dakinsa ita
    kuwa ta kasa koda motsi dan fargabar irin
    zaman da zatayi dashi sai dai ita kuma har
    acikin ranta taji tana tsananin sonsa sannan
    kuma yana burgeta tun ranar farko data fara
    ganinsa ta dade azaune sannan ta tashi ta shiga
    kitchen ta dora abinci akaro na farko tun
    zuwanta gidan domin kullum mummy ce take
    bayarwa ake kawo mata shinkafa da miya ta
    dafa sa'arta daya ta iya girki domin ko agida
    wani lokacin itace take yiwa abbansu girki
    musamman ma idan zaiyi baki na kunya haka ta
    shirya abincinta mai rai da lafiya taje ta jera
    akan dining sannan ta wuce dakinta har yanzu
    bata jin zafin sa sai dai abu dayane ya tsaya
    mata arai auren ramuwar gayyar da yayi da ita
    shine har yanzu yake damunta tana daga cikin
    dakinta ta jiyoshi yana waya amma ba zata
    tantance da mace yakeyi ko da namiji ba abincin
    ya danci kadan sannan ya wuce side din
    mummy tundaga babban falo ya fara jiyo
    muryarsu husna suna cewa wlh mummy yaya
    lamin yafi yaya Abdul iya zabe matarsa tafi Anty
    Kausar kyau daya daga cikinsu yaji tana cewa to
    danma ba kiga gashinta ba ni jiya dana shiga
    dakinta lokacin ta fito daga wanka tsorata nayi
    gashinta fa har kugunta yanda kika san yar
    India murmushi momyn tayi tace ai dama daga
    ganinta zatayi gashi dai dai lokacin ya shiga
    cikin falon mummy suna ganinsa sukayi tsit sim
    sim suka fara kokarin fita suna cewa sannu da
    zuwa yaya lamin side din junada suka nufa suna
    fadin umm su anty junada yau honey ya dawo.
    MACE GUDA DAYA TILO
    ƒ£0⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Suna shiga suka sameta zaune acikin falonta
    tana kallon wani Nigerian film a tashar
    Nollywood zama sukayi suka fara tsokanarta
    yau anty junada ko nemanmu ba kyayi saboda
    yaya yadawo ko? Murmushi tayi tace ku kuka
    sani dai hasna ce tace wai anty junada ke yaya
    yana yimiki dariya husna ce tayi tsagal tace ba
    dolensa ba ita dai bata tanka musu ba haka
    suka karaci surutunsu nan suka zauna har
    magriba sai da sukaji shigowarsa sannan suka
    bar bangaren nata suka nufi nasu. Haka
    zamansu ya kasance Ita dashi kullum tana shiga
    tana gyara masa daki yauma kamar kullum tana
    jin fitarsa ta nufi dakinsa tashiga da toilet tafara
    sai da wankeshi tas sannan ta dawo cikin dakin
    tafara gyarawa ta shareshi tas ta goge tile din
    ta fito da kananan kayansa ta wankesu sannan
    ta fesa air freshener adakin drawer mudubinsa
    ta jawo tana shirya masa wasu takardu da
    tagani ya barbaza akan gado da alama test
    yayiwa dalibansa shine da yagama marking ya
    bazasu anan yatashi ya barsu awurin tana gama
    shiryasu kamar ance buda ta kasan ta jawo ta
    bude me zata gani wani kwali tagani yanata
    kyalli ta dauko tana budawa taga sun zubo tana
    duba jikin kwalin taga an rubuta condom
    gabanta ne yafara faduwa dasauri ta mayar
    masa inda yake ta ajiye ta rufe drawer ta koma
    dakinta innalillahi kawai take fada ba dai lamin
    neman mata yake yi ba? Tambayar da take ta
    yiwa kanta kenan innalillahi wa inna ilaihi raji'un
    zina? Kukane ya subuce mata nan ta zauna ta
    sha kukanta ta more wani kishine ya turnuke ta
    ganin kukan bashine mafita ba yasa ta tashi
    tashiga bathroom ta wanke fuskarta ta fito ta
    tsaya agaban mudubi ta gyara fuskarta fes ta
    fito ta nufi side din mummy tana shiga ta hango
    shi a babban falon yana kishingide yana karanta
    jarida ta gabanshi tabi ta wuce tashiga falon
    mummy ta samesu zaune ita dasu hasna suna
    ganinta suka fara murna oyoyo antynmu yanzu
    muke cewa bari mu tashi muzo tunda ke baki
    shigo ba har yanzu.
    [3/23, 9:51 AM] Ummi A'isha🏻: [3/23, 9:29 AM]
    Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO
    ƒ£1⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Murmushi tayi sannan tace ku dai kuyi shiru
    kawai tunda gashi na zo shikenan ta durkusa
    tana gaida mummy sannan suka dunguma zuwa
    dakinsu su husna anan suka zauna suka fara
    hira sai da rana tayi sannan tafito mummy ta
    hango tana kokarin shiga kitchen ta dora girki da
    sauri ta bita tace mummy me za adora? Cike da
    jin dadi tace jalop rice zan dafa to mummy
    barshi zan dafa cikin jin dadi mummyn tace to
    Allah yayi miki albarka ta juya ta fita daga cikin
    kitchen din cike da jin dadin yadda junada take
    darajata kuma take mutunta ta a falo ta zauna
    wurin lamin tanata yabon junada kafin kace me
    tuni junada tagama girkin ta yi farfesun hanta
    sannan ta hada salad ta zuzzuba su a flasks ta
    zo ta jera akan dining farin ciki ne ya mamaye
    zuciyar mummy, dakin su husna takoma ta
    zauna suka ci gaba da caftarsu ba ita ta tafiba
    sai dare tana zuwa dakinta ta sawa kofarta key
    ta kwanta nan da nan taji bakin ciki ya
    mamayeta sakamakon tunowa da abinda tagani
    adakin lamin wata zuciyar tace yanzu har ya isa
    neman mata? Eh ya isa mana tunda rayuwar
    waje yayi wata zuciyar ta bata amsa dakyar ta
    samu bacci ya dauketa. Ahaka suka zauna har
    ya gama weekend dinsa ya koma kano, kullum
    dakin su husna take wuni idan lokacin girki yayi
    ita zata shiga ta girka musu, suna jin dadin
    zama da ita sosai itama tana jin dadin zama
    dasu mutuka gashi kuma shi kanshi dadyn nasu
    yana ji da ita dan yauma foam ya kawo musu
    na federal university Yola yace su cike su ukun
    zasu fara zuwa makaranta tare. Su hasna
    psychology suka cike ita kuma micro Biology
    zata karanta,shi kuwa lamin yana can kano yana
    shagalinsa yama manta da wata junada tunda
    yatafi bai dawo ba saida yayi 2 weeks sannan
    yazo amma duk da haka junada bataji zafinsa
    ba asalima Allah Allah take yazo ta ganshi tana
    cikin dakinsa tana goge masa takalmansa ya
    shigo ko kallonta baiyi ba ya ajiye jakarsa ya
    shiga bathroom, murmushi tayi ta tashi tafita
    domin ta hada masa abinda zai ci.
    MACE GUDA DAYA TILO
    ƒ£2⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Taliya da macaroni ta dafa masa da miyar
    kwai ta kawo masa kan dining sannan ta fita
    zuwa bangaren mummy, yana fitowa daga
    wanka ya shirya cikin jar riga da wando baki
    yafesa turaren volish mai sanyin kamshi ya fito
    falo abincin data ajiye masa yaje ya buda
    kamshi ne ya bugeshi domin miyar tun a ido ta
    burgeshi tayi yellow tasha curry zama yayi ya
    zuba yaci ya koshi sannan ya fita wurin mummy
    acan ya samesu sunata zuba a babban falo
    amma suna ganinsa suka yi shiru bai kulasu ba
    ya shigewarsa dakin mummy. Sai dare yauma
    takoma side din ta lokacin data shiga yana
    zaune a babban falo yana daddana laptop
    dagowa yayi ya kalleta yace ke kawo min tea to
    ta amsa ta shiga kitchen ta hado masa tazo ta
    ajiye akan dan teburin dake gabansa ta wuce
    dakinta. Dasafe ta tashi ta gyara ko ina tsaf ta
    shiya breakfast sannan ta wuce dakinsa baya
    ciki da alama ya fita gyara dakin tayi sannan ta
    debo kayansa data wanke masa tun jiya tafara
    gogewa tana cikin gugar yashigo ya wuceta
    yashiga wanka bai dade sosai ba ya fito daga
    shi sai gajeren wando kallo daya tayi masa ta
    sunkuyar da kanta kasa ke ina kika ajiye min
    pants dina da kika wanke min? Mikewa tayi
    cikeda jin kunya ta dauko masa ta bashi warta
    yayi sannan ya wuce gaban drawer yafara
    shiryawa.
    [3/23, 9:31 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILOƒ£3⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Kanta yana sunkuye har yagama shiryawa
    yafita daga cikin dakin gugar taci gaba dayi har
    ta goge kayan tas gaba daya ta fito ta shiga
    dakinta tayi wanka tana fitowa ta jiyo hayaniyar
    su hasna acikin falonta ta shirya ta fito wurinsu.
    Ranar Monday da sassafe ya fice ya nufi kano
    ita kuma ta tafi wurinsu mummy tana shiga
    suka fara yi mata albashir da sun samu
    admission har daddy yasa aje ayi musu
    registration dadi taji domin ko ba komai karatun
    zai dan debe mata kewa,aranar ummanta tazo
    mata murna kamar zatayi ihu haka suka koma
    side dinta ta cikata da kayan ciye ciye ita kuwa
    mahaifiyar tata kallon yartata takeyi tare da son
    jin irin zaman da sukeyi da mutanen gidan cikin
    fara'a tace wlh umma zamanmu lafiya dasu
    kowa yana kaffa kaffa dani harta shi kanshi
    daddy bakiga yadda yake kaunata ba kuma shi
    baima cika zama agida ba amma duk lokacin da
    yayo waya sai ya tambayi lafiyata dadi umman
    taji sannan tace to ya zamanku da mijin naki
    kuma? Murmushi nanma tayi tace shima lafiya
    lau muke zamanmu umma yau da sassafe ya
    tafi kano cikin fara'a tace ai mijinki yaron kirki
    ne last week ma yaje ya gaishe mu, amma ina
    masu aikin naki naga kamar babu kowa? Kanta
    ta daga eh wlh umma mummy ta samo min
    guda 3 to gaskiya banida ra'ayi ne tunda aikin
    nawa ba wani mai yawa bane kuma ni in banda
    kwanciya babu abinda nakeyi shiyasa nace gara
    kawai na rinka aikin mijina da kaina ko nafi
    samun lada murmushi umman tata tayi tace
    dakyau gaskiya kinyi kykkyawan tunani Allah
    yavada lada haka suka ci gaba da hirarsu batare
    da umman ta fahimci akwai matsala tsakaninta
    da mijin nata ba, wuni guda umman tata tayi
    amma ko kadan bata fahinci akwai matsala da
    mijin nata ba sai la'asar sannan sukayi mata
    rakiya zuwa airport ta hau jirgi ta tafi bauchi.
    [3/23, 9:35 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILOƒ£4⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Acikin satin aka gama musu registration da
    komai na makaranta dama tuni anfara lectures
    dan haka daddy yace next week sai su fara
    zuwa da kansa ya dauko key din mota sabuwa
    Benz C230 ya bata yace saboda zuwa
    makaranta murna wurinsu ba acewa komai ita
    kanta junadan murna take domin ta daura
    aniyar karatun dagaske bada wasa ba,shi kuwa
    lamin ko weekend dinma bai zo ba saboda yana
    can tareda Mary a kano haka yayi zamansa bai
    waiwayi yola ba. Ranar Monday suka fara
    halarta makarantar su uku husna da hasna
    department dinsu daya ita kadai ce department
    dinta daban haka suka rinka zuwa wani lokacin
    har 2 suke kaiwa a makaranta babu laifi yanzu
    tana dan samun saukin tunanin da yaje
    addabarta. Sai karshen week din lamin yazo
    yola lokacin tana side din mummy suna kallon
    wani Indian film mai suna fashion kallo ya bisu
    dashi yace kullum Ku kenan a kallo kun shiga
    makarantar ma amma bazaku rage kallo ba
    maza dai yarinya ta samo carry over wlh saina
    tattakata sai a sannan junada ta daga kai ta
    kalleshi yana sanye da brown din riga da bakin
    wando fuskarsa sai sheki take tamkar wani
    tauraro bataso ya daina yi musu fadanba domin
    tana son amon muryarsa tana yimata dadi sosai
    dakin mummy ya shigewarsa husna kuwa taba
    baki tayi tace kaji shi ko ina ruwansa itama
    hasna bakin ta taba tace bar masifaffe kawai ai
    kuwa nan da nan junada ta bata fuska tace
    bana son cin fuska gaskiya ya kuke zagin mijina
    agabana? Murmushi sukayi sorry Anty harda
    hada baki hakan da sukayine ya bata dariya
    sosai. A haka sukaci gaba da zama har
    karatunsu yayi nisa alokacin shi kuma lamin ya
    gama service dinsa ya tafi Malaysia ya karbo
    result dinsa yana dawowa ya samu aiki a state
    university yola yafara lecturing tsakanunsa da
    matarsa kuwa sai dai kallo domin har yanzu
    yana nan akan bakansa neman mata kuwa
    yanzu ma yasa kafa.
    Duniyar makaranta littattafan Hausa
    Group Admin
    MACE GUDA DAYA TILO
    ƒ£5⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Haka suka ci gaba da zaman doya da manja
    tsakaninta dashi kullum side din mummy take
    wuni idan babu makaranta idan da akwai kuwa
    tana dawowa acan zasu yada zango ita dasu
    hasna sai dai kullum tana gyara masa dakinsa
    ta wanke masa toilet ta wanke masa kayansa ta
    dafa masa abinci ta ajiye masa amma bata taba
    burgeshi ba asalima shi a matsayin yar aikinsa
    ya ajiyeta. Semester tayi nisa domin har sun kai
    middle karatu sukeyi sosai kuma acikin wannan
    yanayin ne daddy da mummy suka samu visa
    zasu tafi kasar Spain inda daddy din zai halacci
    wani workshop na tsawon sati biyu daga nan
    kuma zasu wuce saudiyya domin gabatar da
    umara dan haka tuni suka fara shirye shiryen
    tafiya su kuma su husna sun gama hado
    kayansu sun dawo sashen junada,washe gari
    sukayi sallama dasu suka tafi suna tafiya suka
    dawo falon junada suka zauna suna hangowa
    yadda zasu kwashe da zaman gidan yaya lamin
    ai kuwa basu dade da zama ba sai gashi fuska
    babu annuri ya shigo ya ce ina take? Tana daki
    husna ta bashi amsa to kice ta kawo min abinci
    ya wuce dakinsa tashi husna tayi tashiga dakin
    lokacin ita kuma junada tagama shiryawa cikin
    wata atamfa yellow dinkin riga da skirt husna
    tayi murmushi kin gama adai dai anty domin
    yanzu yaya yadawo yace ki kai masa abinci to
    ta amsa tafita da sauri tashiga kitchen dambun
    shinkafa tayi da farfesun koda ta dauki juice mai
    sanyi ta nufi dakin nasa yana zaune bakin gado
    daga shi sai gajeren wando yana waya kanta a
    kasa ta isa gabansa ta ajiye farantin ta juya ta
    fice. Suna nan zaune a falon yafito cikin shiga
    mai kyau blue din jeans da pink din riga yayi
    kyau sosai sai kamshin turaren Phoenix ne ke
    tashi ajikinsa ko inda suke bai kalla ba yafice.
    [3/23, 9:51 AM] Ummi A'isha: [3/23, 9:41 AM]
    Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO
    ƒ£6⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Husna ce ta kalli hasna tace tofa ai mun shiga
    uku kuma tunda aka barmu awurin wannan
    mugun hasna tace ai dama wlh da yaya Abdul
    na nan agidansa zamu zauna harararsu junada
    tayi tace ai kuwa da baku isaba wlh suna cikin
    maganar sai gashi sun shigo shida wasu mata
    guda 2 kyawawa dakinsa suka wuce bako sannu
    dama yan matan ba musulmai bane Jim kadan
    sai gashi ya fito ya kallesu daya bayan daya
    yace wadannan abokan aiki nane zasu zauna
    anan dan haka wlh koda wasa naji yarinya ta
    fada idan su daddy suka dawo sai na illata ta
    kuna jina kai suka daga dan duk cikinsu babu
    wacce ta iya magana junada kuwa tafi kowa
    bakin ciki ranta ya gama baci sosai juyawa yayi
    ya koma dakin hasna ce ta mike ta shiga
    dakinsu wanda yake opposite din dakin junada
    husna itama tashi tayi tabi bayanta tana shiga
    tasameta ta rafka tagumi kusa da ita taje ta
    zauna tace hasna me kika fuskanta da wannan
    lamari? Cikin takaici hasna tace ai husna yaya
    lamin dan rainin wayone wai abokan aiki
    wadannan sunyi kama da lecturers? Kawai yan
    matansa ne wlh ni dama nadade da sanin yaya
    lamin yana neman mata cikin bacin rai husna
    tace ai shiyasa kullum nake tausayawa anty
    junada tana mutukar hakuri dashi kuma bata
    taba nuna mana laifinsa ba kullum cikin boye
    sirrinsa takeyi bata taba fada mana tsakaninsu
    ba Allah shiryeshi amin inji husna. Ita kuwa
    junada dakyar ta iya tashi saboda jirin da yake
    dibanta sai yau tasan tana tsananin kishin
    mijinta akan gadonta ta kwanta tafara wani irin
    kuka mai ban tausayi acikin zuciyarta kuwa
    addu'a take masa Allah ya shiryar dashi haka ta
    wuni tana kuka tuni kanta yafara ciwo amma
    haka ta fito ta shiga kitchen ta dafa musu abinci
    ta koma dakinta ranar haka dukansu su ukun
    suka wuni cikin takaici shi kuwa yana can yana
    holewarsa.
    MACE GUDA DAYA TILO
    ƒ£7⃣

    Na
    UMMIA'ISHA
    Wasa wasa tun abin yana basu haushi har ya
    dawo ya daina basu domin yan matan nan sai
    da suka shafe kwana 9 acikin gidan sannan
    suka tafi shi kuwa ko ajikinsa su husna kuwa
    basu isa sun fadi laifinsa agaban junada ba dan
    yanzu zata bata rai taji haushinsu sai dai idan
    sun koma gefe suyita Allah wadai da halin yayan
    nasu ita kuwa junada addu'a kawai take yi Allah
    ya shirya mata shi ya karkato mata da
    hankalinsa kanta. Ranar Monday tunda wuri ta
    tashi ta shirya masa breakfast ta gyara masa
    dakin ta koma ta tashi su husna suka shirya
    suka tafi makaranta suna dawowa suka tarar
    yana fitowa shida wata farar budurwa Christian
    da sauri suka basu hanya suka fita sannan suka
    shiga falon,junada cikin ranta taji kamar taje ta
    shake wannan matar amma babu dama. Aranar
    da daddare yazo da wata daban shi kuma
    sassafe ya fice domin 8 to 10 yake yiwa wasu
    daliban lecture wasu kuma 1 to 2 ita kuwa
    junada saida tagama gyara ko ina sannan ta
    nufi dakin nasa da nufin gyarawa tana shiga ta
    ganta kwance kyakkyawa ce sosai ai nan da nan
    kishi ya cikata duka ta daka mata firgigit ta
    tashi tana mikewa ta kifa mata mari tace dan
    ubanki me ya hadaki da mijina tsorone ya kama
    arniyar tace kiyi hakuri bai cemin yana da mata
    ba, ni nafada miki kuma yau sai na kasheki wata
    kwalbar lemo ta dauka tace zaki kara kula
    mijina? Cikin tsoro tace a'a hakuri ta fara bata
    sosai saida ta Kara wanketa da mari sannan ta
    hankadata waje ta cilla mata jakarta waje ai tuni
    tafice daga gidan aguje ranta babu dadi tagama
    gyara dakin tafice. Haka zaman nasu ya
    kasance har sati 3 tuni an kafe musu time table
    na exam anyi closing lectures din dan haka babu
    inda suke zuwa karatu kawai sukeyi agida.
    [3/23, 9:47 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO..ƒ£8⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Yauma kamar kullum da sassafe junada ta
    tashi tagama gyare gyaren gidan su husna suna
    can suna aikin nasu wato bacci idan suka
    kwanta bacci daga asuba sai sun Kai 12 basu
    farka ba itace take tashi da wuri take ayyukanta
    duka. Wurin 11 tagama komai ta shiga dakinsa
    baya ciki da alama ya fita kananan kayansa ta
    tattara tashiga toilet ta wanwanke sannan ta
    wanke toilet din, tana gamawa tadawo cikin
    dakin tafara gyarashi tana gyaran gado suka
    shigo shida wata arniya siririya baka kyakkyawa
    ya dan saci kallon junadan yaga tayi kicicin
    kunya ya dan ji don baisan tana cikin dakin ba
    kallon yarinyar yayi yace Jen have a sit am
    coming ficewa yayi daga dakin Jim kadan sukaji
    karar tashin motar da alama fita yayi daga
    gidan juyowa junada tayi taga karuwar tasa tana
    gyara fuskarta ajikin mudubi fisgo ta tayi tafara
    wanka mata mari tas! Tas! Tas tace dan ubanki
    zaki kara biyo mijina? Cikin kuka tace no am
    sorry pls tace ba wani hakuri dan ubanki yau
    saina datse miki kafafu tuni Jen ta rude tafara
    bata hakuri fincikarta tayi ta hada da bango ta
    shaketa dai dai nan yashigo dasauri junada ta
    saketa ita kuwa tace kafa me naci ban baki ba
    sai gudu ko sauraronsa batayiba, cike da
    mamaki ya kalli junada yace me kikayi mata?
    Shiru tayi masa taci gaba da aikinta ransa ya
    baci sosai ficewa yayi daga dakin ya koma falon
    ya zauna ita kuwa aikinta tayi tana gamawa ta
    fito ta wuce dakinta.
    MACE GUDA DAYA TILO...
    ƒ£9⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Mamaki ne ya kamashi to me yakori jen?
    Wayarsa ya dauka yafara kiranta tana dauka
    tafara zaginsa tana cewa banza mayaudari
    dama ashe kanada mata shine ka daukeni ka
    kaini gidanka dan matarka ta kasheni ko? To
    daga yau babu ni babu kai macuci kawai ta
    kashe wayarta mamaki ne ya cikashi to me
    wannan yarinyar take nufi? Rannan ma da
    yadawo bai samu Grace ba bayan kuma yatafi
    ya barta adakin da yakirata awaya da kyar ta
    dauka ta zazzageshi wai ba ita bashi domin
    matarsa mahaukaciya ce kashe mutane take
    wato itace take korarsu kenan kodai sonsa take?
    Tashi yayi yabar falon ganin bashida amsar
    tambayar da yayiwa kansa. Ita kuwa ta daina
    ma saka abun aranta addu'a kawai takeyi Allah
    ya shirya shi, yau saura kwana 3 su mummy su
    dawo daga umara har sun fara shirye shiryen
    taryarsu tana dakinta akwance su husna kuma
    suna daya dakin ya shigo ki tashi ki dafa min
    indomie guda 4 da soyayyen kwai ki kawo min
    daki to tace ta mike ta shiga kitchen tana
    mamakin kanta wai yau itace ake juyawa haka
    duk irin gatan ta lallai ta yadda sarki agidan
    wani sarkin bawa ne da wannan tunanin ta
    gama dafawa ta soya kwai guda 6 ta dauki
    cokala guda biyu dan tasan shi kadai indomie
    Hudu tayi masa yawa dan bashida cin abincin
    sosai dakin nasa ta nufa ta kwankwasa shiru
    dan haka kawai sai ta tura kofar tana shiga ta
    hangoshi daga shi sai gajeren wando ita kuwa
    karuwar tasa zigidir take haihuwar uwarta sun
    shagala sai romancing juna suke tuni jikinta ya
    fara rawa ta saki farantin abincin ya zube filet
    din tangaram din ya fashe karar ce tadawo dasu
    cikin hankalinsu tuni ta ruga aguje tabar dakin
    shi kuwa jikinsa yaji yayi masifar sanyi rana ta
    farko da yaji kunyar junada ranar farko da yaji
    ya tsani zina arayuwarsa kuma yaji ta fita acikin
    ransa tashi yayi yace da Agnes ta shirya ta bar
    gidan tambayarsa abinda ya faru tafara wata
    tsawa ya daka mata yace ta fice kawai cikin
    sauri ta shirya ta dauki jakarta ta fita shi kuwa
    kamar wanda aka zarewa laka ajiki duk ya
    sukurkurce.
    Duniyar makaranta littattafan Hausa Group
    Admin
    Ummi A'isha
    MACE GUDA DAYA TILO..
    ƒ£0⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Tana isa dakinta ta kwanta akan gado jikinta
    sai faman rawa yake innalillahi kawai take
    ambata, hayaniyar su husna ta jiyo a falo amma
    bata fita ba tana nan kwance kamar marar
    lafiya, shi kuwa lamin dakyar ya iya tashi yasa
    kayansa ya fito daga falo tajiyo yana tambayar
    su hasna ina take? Tana cikin daki inji su kai
    tsaye dakin ya wuce ya ganta kwance ta
    kudundune kanta ke ki tashi kije ki gyara min
    dakina da kika bata ni fita zanyi yana fadin haka
    ya fita ita kuma tashi tayi tana mamakin shi
    kuwa lamin me yagani ajikin wannan arniyar? In
    banda kashi ita bata ga komai ajikinta ba amma
    dan jaraba irin ta maza shi burgeshi tayi ahaka
    mikewa tayi taje ta gyara dakin ta kunna turaren
    wuta sannan ta rufo kofar ta dawo wajen su
    hasna. Washe gari da wuri ta fito saboda
    yunwar da takeji kanta tsaye kitchen ta wuce ta
    debo ruwan zafi tazo ta hada tea mai kauri ta
    dawo falo tafara sha da niyyar idan ta gama
    zata koma kitchen ta hadawa su hasna da lamin
    nasu, kamshin turarensa tafara jiyowa tuni
    kamshin nasa ya gama rudata ta ajiye kofin
    sakamakon ganinsa da tayi ya fito yana sanye
    cikin suit bakake yayi kyau sosai kallonta ya yi
    sannan yace bani breakfast dina fita office zanyi
    dasauri ta mike ta shiga kitchen ta soya masa
    manyan kwai guda 4 ta debo ruwan zafi a kofi
    sannan ta dauko masa bread ta dawo ta ajiye
    masa ta koma ta dauko butter da yar wukar da
    za ashafa butter din ta dawo ta ajiye ta nufi
    kitchen ke ni zan shafa butter din? Taji yace
    dawowa tayi tazo ta tsugunna ta dauka ta fara
    shafa masa shi kuma ya dauki kwan ya fara ci,
    yan yatsun hannunta ya zubawa ido farare sol
    dasu dogaye miko masa tayi yasa hannu ya
    karba yana mai ci gaba da kallon hannun nata
    tana gamawa ta mike ta koma kitchen.
    Ummi A'isha
    [3/23, 11:54 AM] Ummi A'isha🏻: [3/23, 11:23
    AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO.....
    ƒ£1⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Aiki tafara tanayi tana tunanin abin sonta
    lamin ita dai Allah ya dora mata sonsa tun ranar
    farko data fara ganinsa a makarantar su
    shigowarsa taji cikin kitchen din kamshin
    turarensa shine ya cika mata hanci tuni taji
    jikinta yayi la'asar ta bayanta ya tsaya ya ajiye
    kayan yabi bayanta da kallo sannan ya juya ya
    fita ajiyar zuciya ta saki sannan taci gaba da
    aikinta tana fadin Allah ya kara shirya min kai
    lamin, sai data gama dukkan ayyukan sannan ta
    nufi dakin sa domin gyarawa tana shiga taga
    wata arniya zaune a bakin gadonsa nan da nan
    kishi ya motsa saboda duk a tunaninta adakin ta
    kwana kallonta tayi tana sanye da wata yar
    ficiciyar riga iya cinya kanta taci gashin kanti fal
    dubanta tayi tace sannu amma ya zaki zauna
    tun safe acikin datti washe baki tayi tace no
    zuwana kenan yanzu shima bai san da zuwana
    ba nayi mishi surprise visit ne murmushin
    takaici tayi ta jawo wani karfe tace yau zan
    koya miki hankali jibga mata tayi zata kurma ihu
    ta toshe bakinta ta yar da karfen ta soma gaura
    mata mari tana cewa waya kawoki wurin mijina?
    Yau saina kasheki idanuwan tane suka firfito ita
    kuwa marinta taci gaba dayi saida ta kumbura
    mata fuska sannan ta kaita waje ta cilla mata
    handbag dinta ta dawo taci gaba da gyaran
    dakin aranta tana raya cewa har yanxu ina son
    mijina kuma zanci gaba da sonsa ya Allah ka
    ganar dashi gaskiya tana gama gyaran dakin
    yana dawowa alhalin kuma ba haka ya saba
    yiba idan ya fice wani lokacin sai dare gabanta
    taji yafara faduwa saboda ta tabbata karuwarsa
    ce ta fada masa dukan da tayi mata dan haka
    cikin sauri ta shige dakinta yana shigowa su
    hasna na fitowa falo tambayarsu yayi ina
    antynku? Tana daki suka bashi amsa cikin dakin
    ya nufa tana zaune bakin gado ki fito ki bani
    abinci yunwa nakeji.
    MACE GUDA DAYA TILO...
    ƒ£2⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Yunwa nakeji office zan koma ko sai kin bata
    min rai? Murna ce ta rufeta tafito ta nufi kitchen
    shikuwa mamaki yakeyi wai wannan yarinyar ce
    kiri kiri ta hanashi zama a office domin
    tunaninta daya addabeshi. Gari na wayewa su
    mummy suka dawo dama tayi musu shirye
    shiryen karbarsu tayi girke girke da yan soye
    soyen karbarsu. Da daddare daddy dakansa ya
    shigo bangaren mummy ya kirawo lamin sudai
    suna zaune suna sauraron abinda zai faru cikin
    fada daddy yafara cewa lamin baka kyauta
    mana ba yanzu ashe dama baka da mutunci?
    An tabbatar min da cewa kana kawo mata gidan
    nan da bama nan cikin sauri junada tace a'a
    daddy karya ake yi masa abokan aikinsa ne aka
    kawosu basu samu dakiba to shine ya kawo su
    nan kafin su samu daki kuma saida ya fada
    mana nida su husna cewa zasu zauna kafin a
    sama musu masauki sannan kuma daina shiga
    dakin yayi har sai da suka tafi cikin mamaki
    yabita da kallo su hasna kuwa shiru sukayi
    domin sun san wannan maganar ba gaskiya
    bace kawai ta fadi hakane danta kareshi amma
    ba wani abokan aiki girgiza kai daddy yayi yace
    shikenan Allah ya rufa asiri suka amsa da amin
    sannan dadyn yatashi ya koma sashensa shima
    sashensu ya tashi ya tafi sai faman cika yana
    batsewa yake.
    MACE GUDA DAYA TILO...
    ƒ£3⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Suna nan zaune a falon mummy, mummy ta
    fiddo musu da tsarabarsu ta basu kowa jaka
    guda ta ciko masa da kaya, nan suka baje
    kayan kowa yana ganin nasa sai murna sukeyi.
    Shi kuwa lamin yana can dakinsa yanata
    tunanin me junada ke nufi? Anya kuwa yarinyar
    nan bata fara sonsa ba? Xumbur ya mike ya
    nufi sashen mummy ya taradda su yanda ya
    barsu mummy dan Allah baku dawo da maganin
    ciwon kai ba? inajin akwai junada ya kalla ki
    kawo min ina daki, mummy ce ta shiga dakin da
    kanta ta debo mata maganin ta bata, mikewa
    tayi ta nufi sashensu ta dauki ruwa a kofi marar
    sanyi tana shiga dakin ta sameshi tsaye abinka
    ga lecturer ansaba tsaiwa mika masa ruwan tayi
    bai karba ba, yace kya iya zubarwa dan ba shine
    a gabana ba, agidan uban wa kika zama matata
    da zaki rinka korar min yanmata? Ai nafada miki
    ni ban daukeki a matsayin mata ba, a yar aiki na
    ajiyeki mamakine ya kamata lallai wani mutumin
    ba ayi masa gwaninta yaci gaba da cewa banda
    ke shasha ce kuma munafuka ina ruwanki da
    sha'anina? Cikin bacin rai ta kalleshi gaka nan
    babban munafuki mai sabawa Allah da
    manxonsa dan nace ni matarka ce shine ina
    nufin sonka nake? Allah ya sawwake me zanyi
    da mazinaci, kazami mai bin yayan arna? Nayi
    hakane dan na kareka daga masifar zina amma
    ba don ina sonka ba ko kana nufin ban san illar
    shaidar zir ba? Nasani amma nayi don na
    tseratar da kai daga fushin iyayenka dan na lura
    kana da karancin ilimin addini baka san hukuncin
    mazinaci ba taja wani dogon tsaki ta juya tafice
    dakinta taje ta kwanta tafara kuka sam bata so
    haka ta faruba taso ace yanda ta sauke duk
    wani girman kanta take binshi sau da kafa
    shima yayi hakuri ya karbeta a matsayin
    abokiyar rayuwa kuka takeyi sosai. Shi kuwa
    yana nan tsaye inda ta barshi kamar dashen ice
    ya kasa koda motsi maganganunta ne kawai ke
    masa yawo a kwakwalwarsa abu 3 ne yafi bata
    masa rai kalmar data kirashi da ita ta jahili da
    kuma kiransa da mazinaci da tayi sannan cewa
    me zatayi dashi yafi komai daga masa hankali
    da bata masa rai, dakyar ya iya daga kafarsa ya
    isa bakin gadonsa ya kwanta kansa sai zugi
    yake masa kamar zai rabe gida 2.
    [3/23, 11:25 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO...ƒ£4⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Kwana 2 yayi yana jinyar maganganunta
    kuma tun daga ranar bai Kara yadda sun hadu
    ba abinci ma idan ta ajiye masa baya ci yanda
    ta ajiye kayanta haka zata dauka bai ko buda ba
    abin duniya ya isheta, bayan ta gama ayyukanta
    tazo ta tsaya ajikin window ta daga labule lamin
    ta hango yana motsa jiki afilin wasa yasa farar
    riga irin ta yan ball da wandonta yasa farin
    takalmi combos yanata buga kwallo shi kadai
    nan ta tsaya tana ta kallonshi har yagama ya
    nufo cikin falon labulen ta saki ta nemi wuri ta
    zauna a bakin gado su husna ne suka shigo
    hasna tace ah anty junada wannan rigar fa?
    Hararsu tayi tace ba ason sa ido da sauri husna
    tace gaskiya rigar tayi kyau kamar shimi amma
    har gwiwa take shigowar lamin ce ta katse
    musu maganar yabi junada da kallo ita kuwa da
    sauri ta jawo hijab ta saka su hasna ya kalla
    yace yaran nan baku da kirki kwana biyu banida
    lafiya amma ko ku dubani cikin sauri sukace wlh
    yaya bamu sani ba eh amma wadda kuke tareda
    ita ai tasani juyawa ga junada sukayi suna cewa
    amma anty baki kyauta ba kallo tabishi dashi
    yayi kyau sosai yana sanye cikin riga t. Shirt
    brown da jeans blue yanata kamshin turaren
    Phoenix kallonta yayi yace zakizo ki bani abincin
    ko kuwa? Dasauri ta mike ta shiga kitchen ciki
    yabita yana tsaye yana kallonta tana zuzzuba
    masa abincin har tagama ta dauko zata fito
    hanya yabata amma yana tsaye a bakin kofar
    tsayawa tayi tace zan wuce to ki wuce mana ko
    na hanaki ne? Ahaka ta wuce amma dole saida
    ta dan bugeshi sannan ta iya wucewa bayanta
    yabi har suka isa dining area din.
    [3/23, 11:40 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TIILO..ƒ£5⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Kallo ya ringa binta dashi har ta gama
    zuzzuba masa ta ajiye masa ta wuce dakinta
    murmushi yayi yafara ci. Wasa wasa sai jinsa
    yayi ya wayi gari da matsanancin son junada
    kuma tun ranar data gaggaya masa
    maganganun nan yaji zina ta fita daga ransa
    baya sha'awar aikatata dan haka tuni yafara
    neman gafarar ubangiji ba dare ba rana. Gaba
    daya sonta yagama shigarsa ta ko ina bashi da
    buri illa kasancewa da ita dan haka ya daura
    aniyar nuna mata so afili tare da bin duk wata
    hanya domin yasamu ta shaku dashi, yau sai 5
    yadawo domin meeting sukayi kansa tsaye ya
    wuce side dinsu amma ya tarar bata nan ya
    tabbata tana wurin mummy dan haka ya nufi
    can din yana shiga ya tarar da mummy a
    babban falo tana waya ita kuma dama yaji
    motsinta a kitchen dan haka kitchen din ya bita
    ya taradda ita tana fere doya kamshin turarensa
    kawai taji tasan yashigo tsayawa tayi cak daga
    aikin da take bayanta ya karaso yazo ya tsaya
    ahankali tamkar mai yin rada yace wai ni
    meyasa duk abinda kikeyi daga kin ganni sai ki
    daina sai kace wani dodo? Saboda ina sonka
    tafada acikin zuciyarta amma a fili shiru tayi
    bata amsa masa ba, da rana me kuka dafa?
    Tuwon shinkafa ta bashi amsa yanzu kuma me
    zaki dafa? Soyayyiyar doya da miyar koda
    murmushi yayi to ni yanzu me zaki bani? Dan
    yunwa nakeji babu abinci amma akwai snacks
    to kawo min snacks din da juice tana jiyowa
    sukaci karo sorry ya fada tareda ja baya ya
    koma falo murmushi junada tayi tace Allah
    yakara shirya min kai lamin yana zuwa ya zauna
    kusa da mummy hayaniyar su husna ya ji a
    dayan falon ya kalli mummy me yaran nan
    sukeyi ne? Kallo mana mummy ta bashi amsa
    murya ya daga hasna kuzo nan suna zuwa ya
    fara masifa wato ku baku da aiki sai kallo ko?
    Kun bar junada ita Kadai da aiki kuna jira ta
    gama ta kawo muku kuci ko saboda ga baiwa?
    To wlh baku isaba kune zaku rinka girki ba
    matata ba ku tashi ku shiga kitchen ku karasa
    aikin da takeyi tashi mummy tayi tana fadin
    dakyau ka kyauta yara yan mata dasu amma ba
    su iya girki ba idan akayi aurensu ya zasu yi ta
    shigewarta dakinta su kuma su hasna suka
    shiga kitchen juyowa yayi ga junada wadda tun
    dazu take rike da kaya a hannu tana jiran ya
    karba.
    MACE GUDA DAYA TILO..
    ƒ£6⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Mika masa tayi ya karba yana cewa kar ki
    kara yi musu girki a marerece tace ai basu iya
    ba kallonta ya sakeyi yace karya suke sun iya ki
    rabu dasu dolensu suyi falon taga yayi gaje gaje
    kamar ba agyara ba dan haka tsayawa tayi
    tafara gyara falon ahankali yafara binta da kallo
    wannan yarinyar gaskiya kyakkyawa ce ta ajin
    karshe sai wanda yake kusa da ita ne ma zaifi
    tabbatar da hakan ta hadu ta ko ina da haka
    yagama cin snacks din yatashi ya fice ya nufi
    side dinsu ita kuwa dama duk a takure take
    yana fita ta tashi ta shiga kitchen wurinsu
    husna. Sai dare tabar side din mummy tare dasu
    hasna domin har yanzu basu dawo sashen
    mummy ba sanda suka shiga yana falo yana
    kallo sannu yaya su hasna suka fada suka shige
    kai kuzo nan ya fada jiyowa sukayi suka dawo
    junada ya kalla wannan yaran har yanzu anan
    suke kwana? Kai ta daga masa tace eh kallonsu
    yayi to wlh kun kusa komawa inda kuka fito
    dalla ku wuce ku bawa mutane waje da sauri
    suka wuce ya kalli junada kawo min ruwan zafi
    amma empty kar kisa milk to ta amsa masa ta
    shiga cikin kitchen ta hado masa ta kawo masa
    rissinawa tayi ta mika masa karba yayi yana
    kallon yan yatsunta wanda suke tsananin
    burgeshi tana bashi ta wuce dakinta. Washe gari
    da wuri ta tashi ta gama abubuwan da za tayi
    ta shirya domin ranar zasu fara exam tun 8:30
    suka tafi lokacin ko tashi daga bacci baiyi ba
    lokacin data shiga dakinsa kwance ta ganshi
    daga shi sai gajeren wando ko riga babu
    ajikinsa,ya kure A. C baccinsa yake hankali
    kwance, kallonsa ta tsaya ta farayi fatarsa sai
    sheki take kamar ta mace da gani zatayi laushi
    ko ina najikinsa gashi ne ya kwanta luf luf wani
    irin kyau taga yayi mata sleeping beauty ta fada
    ahankali ta fice daga dakin. Shi kuwa lokacin da
    ya tashi ya shirya ya fito sai yaji falon tsit da
    alama sammako sukayi zuwa makaranta.
    Ummi A'isha🏻
    [3/23, 11:54 AM] Ummi A'isha🏻: [3/23, 11:45
    AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO

    ....ƒ£7⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Falon ya fito yakarasa kan dining yaga flasks
    a jere, yafara budewa soyayyen dankali da kwai
    yaga sai kamshi yake, ya bude dayan farfesun
    kaji ne shima kamshine kawai ke tashi duk
    abinda tasan yana bukata ta hada masa nan ya
    zauna ya cika tumbinsa sannan ya nufi cikin
    dakinta yana shiga yaji kamshin room freshener
    dana turaren wuta sun hadu sun doki hancinsa
    dakin nata yafara kallo komai tsaf tsaf babu
    datti ko daya gefen gadonta yaje ya kwanta
    aransa yana tunanin cewa ya kamata ya ajiye
    duk wani girman kansa ya rungumi matarsa ya
    nuna mata soyayya dan tabbas yar halak ce duk
    matsayinta da mukamin mahaifinta amma ta
    kaskantar da kanta take yi masa bauta har
    kayansa ta ke wankewa ga wulakancin datake
    fuskanta daga wurinshi amma duk ta jure wani
    irin juyi yayi akan gadon yace nayi alkawari sai
    nayiwa junada abinda zata soni, zata kaunace ni
    tashi yayi yakoma dakinsa domin duk ba yajin
    dadin jikinsa sakamakon rashin ganin junada
    dan haka yau bazashi aiki ba. Yana nan kwance
    ya saka fari ya saka baki har ya kwashe awanni
    bai ankara ba ya jiyo hayaniyarsu acikin dakin
    junada, tashi yayi ya nufi dakin nata lokacin
    hasna tana daya dakin tana wanka ita kuma
    husna tana tsaye tana sanye da wata doguwar
    shimi ta bawa kofar shigowa baya tana shirya
    lecture note dinta ita kuma junada dogon wando
    ne ajikinta da bra tana zaune akan gado tana
    facing din kofa ta sunkuyar da kanta tana duba
    questions paper din su husna gaba daya
    hankalinta yana kan question paper din yana
    shiga ya ganta yasalam ya fada sadaf sadaf ya
    juya da niyyar ficewa amma sai aka samu akasi
    kafarsa ta bugi kofa dago kanta tayi tana
    dagowa suka hada ido wata kunya ce ta
    lullubeta shi kuwa cewa yayi sorry you are
    changing? Ya fice daga dakin hankalinsa a tashe
    acikin ransa yana cewa lallai ashe yarinyar nan
    lullube take da baiwa iri iri shiyasa take yanga?
    Lallai da yaso tafka babban kuskure a
    rayuwarsa, ita kuwa junada haka kawai ta kasa
    jin zafinsa amma taji wata azababbiyar
    kunyarsa ta kamata.
    MACE GUDA DAYA TILO...
    ƒ£8⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Tun daga lokacin ta daina yarda su hadu,
    wasan buya suka shiga tun bai gane ba har
    yagano kunyarsa take ji murmushi kawai yayi
    yace yaro yaro ne. Ahaka ahaka har suka kusa
    gama exam dama shi kawai kyaleta yayi tagama
    exam din lokacinne zai fito mata da manufarsa a
    fili, da daddare yashigo a babban falo ya iskesu
    suna cin abinci suna kallon wani Nigerian film
    mai suna i promise kowa rike da filet dinta a
    hannu gaba daya hankalinsu ya tattara akan
    film din ahankali yazo kusa da junada ya zauna
    batare da sunji motsin sa ba magana yayi yace
    sannunku sarakan kallo gaba dayansu babu
    wadda bata tsorata ba dan sam basuji shigowar
    sa ba kallo junada ta fara binsa dashi yayi kyau
    sosai rigar jikinsa maroon colour an zana
    tsintsaye guda uku ajiki an rubuta Angry Birds
    brown din jeans yasa kamshin turaren sa kamar
    kullum ya baibaye wurin,husna ce tayi dariya
    tace gaskiya yaya ka bamu tsoro wlh junada ya
    kalla wadda har yanzu itama shi din take kallo
    murmushi yayi yace ga babbar matsoraciya nan
    wadda take neman cinye ni da ido dariya suka
    sa ita kuwa murmushi tayi ta dauke kanta daga
    kallonsa abincin nata ya dauka yace matso muci
    nima yunwa nake ji kallonsa tayi tace ni na
    koshi kaci sai in karo maka tsareta yayi da ido
    tamkar mai yin rada yace wlh baki isa ba sai
    munci abincin nan tare kafada ta make ahankali
    ahankali yafara matsowa har yazo kusa da ita
    sosai ya kamo hannunta daga shi har ita wani
    bakon al'amari ne ya ziyarce su wani irin yarr
    taji ajikinta, su husna kuwa tsayawa sukayi suna
    ganin ikon Allah, ganin bazata ci ba yasashi
    kwanto da ita jikinsa ya debo yana shirin bata
    tamkar wata jaririya kunya ce ta kamata ganin
    su hasna na kallonsu shi kuwa yama manta
    dasu na wurin ganin taki ci yasa yajiyo asannan
    ne ya gansu korarsu yayi yace kai ku bar nan da
    sauri suka mike suka shige daki suna shigewa
    ya jiyo gareta yasa tattausan hannunsa ya
    kamo hannunta wanda ya dade yana burgeshi
    ahankali yafara murza yan yatsunta acikin
    hannunsa wani irin taushi da laushi yaji a
    hannun nata tuni ya shagala yama manta da
    batun abinci.
    [3/23, 11:50 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO...ƒ£9⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Ahankali ta zare hannun nata daga cikin
    nasa ta kalleshi tace to kaci abincin kace yunwa
    kakeji kallonta shima yayi idanuwan shi sun
    canza launi yace ai nace miki tare zamuci tashi
    tayi taje cikin kitchen ta zubo abincin ta dawo
    wurin shi ta ajiye akan stool din gabansa
    kallonta yayi yace to muci kinga cokalin guda
    daya ne don haka sai muyi kama kama zama
    tayi a kusa dashi abincin ya fara ci ya miko
    mata cokalin karba tayi itama tafara diba tana
    ci shi kuwa gaba daya hankalinsa yana wajenta
    ahaka har suka gama cin abincin mikewa tayi
    da nufin zuwa ta dauko musu ruwa da sauri ya
    kamo hannunta yace barshi na dauko mana a'a
    ka barshi zan dauko no barshi kawai mikewa
    yayi yaje fridge ya dauko musu ruwan da kofi ya
    dawo wajenta yace zakisha da kanki ko na baki
    a baki? A'a zan sha da kaina tsiyayo mata yayi
    ya mika mata ta karba tasha sannan ta mika
    masa shima yasha, mikewa tayi tace zan shiga
    daki binta yayi yace to muje tana gaba yana
    biye da ita har cikin dakin a gefen gadonta ya
    xauna ita ma zaman tayi domin a takure take
    gashi tana son tayi wanka amma bazata iya
    tashi tashiga a gabansa ba.
    MACE GUDA DAYA TILO...
    ƒ£0⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Tashi yayi yace to sai anjima Allah ya jima
    damu tafada a hankali fita yayi daga cikin dakin
    ya nufi dakinsa ita kuma wanka ta tashi ta
    shiga tana fitowa ta ganshi tsaye daga shi sai
    gajeren wando da farar best kallonta yafara yi
    sosai daga ita sai dan guntun towel, gashin
    kanta har kugunta sai faman kamshin mai dadi
    takeyi na sabulun da tayi wanka dashi yaya
    lamin me kake so? Ta fada cikin rawar murya
    kamar wanda yake koyon magana yace ruwan
    wanka zaki zo ki hada min to ina zuwa ta bashi
    amsa acikin zuciyarta kuwa cewa take aikin
    nawa ya karu kenan tunda yanzu har dasu zuba
    ruwan wanka, tsaye ya tsaya mata yaki fita
    jiyowa tayi tace ina zuwa shiryawa zanyi
    kallonta yayi sannan yace to shirya mana ko na
    hanaki ne? Ganin bashida niyyar fita yasa ta
    tattaro gashin kanta ta tufke tamkar gammo a
    kunyace ta dauki dogon hijab ta sa tazo zata
    wuce jawota yayi yace tsaya mana madam kisa
    kayanki mana a'a sai na dawo zan sa to
    shikenan muje wucewa tayi izuwa dakin nasa ta
    shiga bathroom ta hada masa ruwan wanka
    harda turaren wanka ta zuba masa ta fito
    lokacin yana waya sunan Jen taji ya ambata
    dan haka ba tayi wata wata ba ta fice daga
    dakin cikin sauri zuciyarta sai faman tafarfasa
    takeyi wato arnan nan ba zasu kyale mata lamin
    ba ko? Allah yasa yarinya tayi gangancin zuwa
    mata gida wlh sai ta raunata ta da wannan
    tunanin ta shitya cikin rigar baccin ta ja mai
    kyan gaske ta jawo hand out dinta ta soma
    karantawa domin tana da exam gobe dama guda
    2 ne suka rage mata. Washe gari ta tashi ta
    hada breakfast ita dasu husna dankali da kwai
    ta soya musu shi kuma lamin plantain da kwai
    ta soya masa tayi masa farfesun kayan ciki ta
    zuba masa ruwan zafi a cikin flask tazo ta jera
    akan dining ta nufi dakin su husna taje ta taso
    su agurguje suka shirya suka fito amma sai da
    junada ta leka dakin lamin inda yake kwance
    yanata shakar baccinsa da sauri taja masa
    kofar ta fita cikin sauri suka shiga sashen
    mummy suka gaidata sannan suka wuce
    makaranta.
    Ummi A'isha🏻
    [3/24, 12:34 PM] Ummi A'isha🏻: [3/24, 10:11
    AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO..
    ƒ£1⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Karfe 9 ya tashi yayi wanka yafito cikin
    bakaken suit wanda sukayi masa kyau sosai,
    kan dining yaje ya xauna yayi break yana
    gamawa ya shiga dakin junada yauma kamar
    kullum dakin a tsaftace yake sai kamshi ne yake
    tashi fitowa yayi ya nufi side din mummy ya
    gaisheta sannan yatafi office. Yau tun 1 suka
    fito daga paper da wuri suka dawo gida su
    hasna daki suka shige suna ramuwar bacci ita
    kuwa junada kitchen ta fada tafara kacaniyar
    hada abincin rana inji turawa sukace lunch, faten
    doya da danyen kifi tayi tana gamawa tashiga
    wanka yauma tana fitowa ta ganshi a tsaye
    kamar jiya sannu da zuwa tace dashi yawwa
    sannu ya amsa mata ganin kallon da yake mata
    yasa tayi saurin sunkuyar da kanta kizo kibani
    abinci amma bari nima naje nayi wanka kafin ki
    gama shiryawa ya juya yafita, agurguje ta shirya
    cikin wani bakin lace mai digon pink ajiki anyi
    masa zanen fulawa ajiki dinkin riga fitet da skirt,
    turaren urban woman shine turarenta ta feshe
    jikinta ta nufi falo tana fitowa shima yana fitowa
    yayi wanka ya canza shiga cikin wata riga
    purple colour anyi zanen heart kanana an rubuta
    cute style a tsakiya da wando brown, gayen nan
    akwai iya daukar wanka tafada acikin zuciyarta
    kujera yaja ya zauna ta zuba masa abincin ta
    koma falon ta zauna tana hango shi yana cin
    abincin shi kuwa mamaki yakeyi wai duk lokacin
    da yarinyar nan take kusa dashi sai ya tsinci
    kansa cikin farin ciki amma da zarar bata nan
    sai ya samu kansa cikin tashin hankali tab!
    Allah mai yadda yaso.
    MACE GUDA DAYA TILO...
    ƒ£2⃣

    Na
    UMMI A'ISHA
    Ahankali ahankali yake cin abincin har ya
    gama, wayoyinsa ya tattara yataso daga dining
    area din cike da ladabi tace yaya lamin dama
    ina son yin magana dakai, kujerar dake kusa da
    ita yazo ya zauna yace ina sauraronki dama dan
    Allah idan nagama exam ina so kabarni naje
    bauchi kallonta yayi yace me akeyi? Babu
    abinda akeyi ta fada tana wasa da yan yatsun
    hannunta wani hamshakin murmushi yayi
    sannan yace to idan kin tafi ni kuma ki barni
    dawa? Kiyi hakuri zakije bauchi amma ba yanzu
    ba kinji? Kai ta daga tace to shikenan a falon
    tabarshi ta shiga dakinta, yana nan zaune har
    su hasna suka fito harara yafara aika musu da
    ita sannan yace wato baku ji abinda nace muku
    ba ko? Allah yabaku sa'a tashi yayi ya nufi side
    din mummy. Washe gari suka gama exam sun
    samu hutu harna 3 weeks dan haka yanzu sai
    zaman gida babu inda suke fita shima lamin
    hutun sukeyi dan haka kullum yana gida, gaba
    daya ya canza ya daina shan kunu da babbata
    rai yana bin duk wata hanya da zasu shaku da
    junada kuma yana kokarin kyautata mata a
    kowanne lokaci,yauma tana kitchen tana girka
    abincin dare yashigo su husna kadai yaga a falo
    suna aikin kallon wani American film mai suna
    prison break ko magana baiyi musu ba ya wuce
    kitchen din lokacin daya shiga tana tuka tuwon
    semo vita ahankali ya lallaba ya rufe mata ido
    tana jin hannunsa tasan shine domin komai
    nasa kamshi yake na turarensa, murmushi tayi
    tace yaya lamin murmushi shima yayi yadawo
    kusa da ita yace sannu da kokari yawwa sannu
    da zuwa tafada tana kwashe tuwon kawo na
    kwashe miki yafada yana kallon fuskarta a'a ai
    baka iya ba tafada waya gaya miki? Ki tambayi
    mummy kiji idan ban iya ba a'a ni basai na
    tambayi mummy ba su hasna zan tambaya to ai
    lokacin da nakeyi su husna basu da wayo a'a to
    duk yadda akayi baka iya ba na iya mana ko
    lokacin da nake Malaysia nine nake girki na ba
    girki kakeyi ba take away kake ci ai nasani a'afa
    kar kisa nayi fushi gobe kina tashi kiga nagama
    shirya breakfast hmmm da kuwa kaga nafi yarda
    da abinda ka fada uhm kinga zaki sa yau naki
    yin marking din papers din dalibai na tunda kince
    ban iya tuwo ba a'a wasa nake ka iya tuwo
    harda miya daidai lokacin tagama kwashe tuwon
    taje ta sauke miyar danyar kubewar data yi ta
    kalleshi to idan bakayi wa dalibanka marking ba
    yaya zakayi dasu? Kowa yasamu carry over
    yafada yana ficewa daga cikin kitchen din.
    [3/24, 10:21 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO..
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£3⃣

    Bayanshi tabi da kallo tana murmushi saida
    tagama shirya komai acikin flask sannan ta
    debo ta kawo kan dining ta jajjera ta karasa
    wajen su husna wanda suke zaune sun kurawa
    tv ido suna kallo, gefensu taje ta zauna itama ta
    fara kallon, lamin ne ya fito shima yazo gefenta
    ya zauna daga shi sai short nicker da farar riga
    body hug laptop dinsa ya ajiye akan Stoll din
    dake gabansa ya miko mata wata takarda ungo
    rinka fado min mark din ko wanne dalibi karba
    tayi tafara karanto masa kallonsa tayi yanzu fa
    muma da dalibanka ne tsaf zaka bamu carry
    over ko? Kwarai kuwa shi yafi komai sauki ma
    musamman ma wadannan yaran masu masifar
    kallon tsiya murmushi tayi ta kalleshi ya
    sunkuya ya dukufa yana daddana laptop din
    fuskarsa dauke da murmushi fado min mark din
    Khadija Aminu 25 a'a ban yarda dakeba sai dai
    35 don yarinyar tanada kokari kusanma tafi duk
    matan ajin kokari ras taji gabanta yafadi to ko
    itama budurwarsa ce? Tafada acikin ranta kin
    san ku mata baku fiya karatu ba shiru tayi masa
    bata bashi amsa ba shi kuwa bai ma san Kalmar
    daya fada ya bata mata rai ba da haka suka
    gama fuskarta babu walwala shima saiya samu
    kansa cikin damuwa, kiran sallar magribar da
    suka jiyo ana kwallawa a masallacin gidan ne
    yasasu tashi gaba dayansu,nan yabar kayan
    aikin nasa yashiga dakin junada a bathroom
    dinta yayi alwala sannan yafito ya tafi
    masallaci, abinda yake Kara burge junada kenan
    domin sam lamin baya wasa da sallah, yana
    fitowa daga masallaci sashen daddy yawuce
    anan ya taradda mummy murmushi yayi yace
    mummy kema nan kika taho? Dariya tayi tace to
    ai babana kune kuka kwashe min abokan hirar
    tawa sai asannan daddy yayi magana yace to
    shi basai yana zuwa yana tayaki hirar ba zama
    yayi akusa da daddy yace to ai sai nazo indai
    mummy tace nazo din, ko cewa tayi nadawo
    gaba daya ma sai nadawo dariya sukayi gaba
    dayansu daddy yace ina matar taka take?
    Kwana 2 ban ganta ba amma ina ganin girkinta
    kullum murmushi mummy tayi tace ai gaskiya
    yayi dacen mata yarinyar nan karfi da yaji ta
    hanani yin girki kullum sai dai ta dafa ta kawo
    min ta dauke ni tamkar mahaifiyarta Allah yayi
    mata albarka shidai lamin shiru yayi amma har
    cikin ransa yaji dadyn yabon junada dasu daddy
    sukayi dama yasan dole su mummy su sota
    domin ko acikin yayansu sunfi sonshi,son da
    suke yi masa nema ya shafi matarshi.
    MACE GUDA DAYA TILO..
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£4⃣

    Anan ya zauna har saida aka kira sallar isha
    sannan suka tafi masallaci shida daddy, yana
    fitowa daga masallaci ya wuce side dinsu nan
    ya taradda su sun baje suna cin tuwo gaban
    junada ya je yasa hannu acikin kwanonta yafara
    cin tuwon sudai su husna mamakin yayan nasu
    sukeyi kwana biyu domin duk ya canza sai
    tattalin matarsa yake gamida tarairayarta
    murmushi yayi mata yace gaskiya miyar nan
    tayi dadi itama murmushin tayi tace ko? Eh
    mana ai tayi dadin da bazai misaltu ba gobe ma
    kiyi mana ita kin san ita kubewa tanada
    mutukar amfani ajikin dan adam likitoci sun
    tabbatar da haka dariya tayi tace to kai kuma
    yaushe kabar lecturing ka koma doctor? Ranar
    da kika bar daliba kika koma noman kubewa
    dariya tayi masa sosai sannan tace gaskiya ya
    kamata nasa maka waigi dan naga alama santi
    kake murmushi yayi ai tuwon naki ya kai
    matsayin da za ayi masa santin yanzu daddy
    ma nasan yana can yana santin wannan miyar
    kubewar hmmm kai dai tunda kayi shikenan
    yana koshi ya mike idan kin gama ki shigo min
    da laptop dina da sauran kayan cikin daki to ta
    amsa masa dakinsa ya wuce yaje ya kunna
    labarai a BBC yana kallo sai wurin 9 sannan
    tashiga dakin nasa da laptop din a hannunta ya
    baje akan gado yana kallo daga shi sai gajeren
    wando idonta ta sauke kasa batare data kalleshi
    ba tace ga kayan naka ajiye anan kishiga
    bathroom ki hada min ruwan wanka, wanka
    zanyi ajiyewa tayi ta shiga cikin bathroom din
    sai data dan wakeshi tafesa air freshener mai
    kamshi sannan ta hada masa ruwan wankan ta
    fito na zuba maka to ki jirani na fito sai mu
    karasa wannan aikin ko? Tom ta nemi wuri ta
    zauna agefen gadon bai dade sosai ba yafito ya
    sameta zaune inda ya barta.
    MACE GUDA DAYA TILO...
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£5⃣

    Bakin gadon shima yaje ya zauna ya kamo
    hannunta ya rike cikin nasa junada ita dai shiru
    tayi tana ganin ikon Allah murmushi yayi ya dan
    kalleta yace junada kalleni kin kallonsa tayi
    magana ya sakeyi ki kalleni junada ni mijinki ne
    abokin rayuwarki, komai da kikaga yana da
    sanadi kuma akwai yadda yake zuwa yanzu ki
    tashi kishiga toilet ki dauro alwala kizo mu
    gabatar da sallar ma'aurata tunda kin korar
    mun yan mata kinga sai ke ki dauki dawainiya
    ta dam! Taji gabanta ya fadi me lamin yake nufi
    ta tambayi kanta dubansa tayi cike da mamaki
    ta fizge hannunta daya rike cikin nasa tace
    ma'aurata? A ina na zama matarka? Ta ina
    muka zama ma'aurata? Kamanta abubuwan
    daka fada a baya? Kai da bakinka kace ba ka
    daukeni a matsayin mata ba a yar aiki ka
    ajiyeni, dan haka ina son kabarni a matsayin yar
    aikin kamar yadda zuciyar ka ta kudurta tun
    farko kar ka canza min matsayi daga yar aiki
    kuma yanzu duk abinda zaka fada bazai yi tasiri
    agareni ba saboda nasan ba gaskiya bane
    kafada ne kawai saboda ka cimma wata manufa
    taka tana kaiwa nan ta tashi fuuuuu! Tafice ta
    bar dakin shi kuwa lamin yakasa koda motsi
    dama yasan dole sai haka ta faru tsakaninsu
    duba da yadda haduwarsu ta kasance tun
    farko,wani guntun tsaki yaja to ita wannan
    yarinyar me takeso tace? Nufinta ba sonta yake
    yiba kawai sha'awarta yake? Mts dama haka ita
    zatayi tunani gani zatayi kamar sha'awarta nake
    dan haka da zarar na cika burina zan daina
    kulata alhalin kuma ba haka bane alokacinne ma
    zanfi kulawa da ita zanfi nuna mata tsantsar
    soyayyar da nake yimata, zan nuna mata kauna
    wacce bata samu ba afarkon aurenmu yafada
    acikin zuciyarsa.
    UmmiA'ishah
    [3/24, 12:34 PM] Ummi A'isha🏻: [3/24, 10:28
    AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO...

    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£6⃣

    Ji yayi zuciyarsa ta fara tafarfasa kamar ana
    hada mata wuta lallai ma yarinyar nan to itada
    ahaka zasuyita zama? Wannan ma ai shirme ne
    kuma ba mai yuyuwa bane tunda shi yanada
    bukata ita kuma ta tsare ta kasa ta hanashi
    kula ko wacce mace sai ita kadai MACE GUDA
    DAYA TILO tashi yayi yafara zagaye dakin nasa
    yayinda bacci kuma yayiwa idanuwansa kaura.
    Ita kuwa junada tana zuwa daki tafara godewa
    Allah domin ta san yafara amsar add'arta tunda
    gashi har lamin yafara nuna son kasancewa da
    ita ina sonka lamin tafada acikin zuciyarta wani
    murmushi tayi sannan tace zan mallaka maka
    kaina amma ba yanzu ba sai lokacin dana
    tabbatar da ka gama kamuwa da ciwon sona
    kagama yarda da cewa nikadai ce MACE GUDA
    DAYA TILO acikin zuciyarka da wannan tunanin
    ta tashi tayi shirin bacci tayi kwanciyarta ba
    tare da damuwar komai ba shi kuwa lamin yana
    can yana ta faman sintiri atsakar dakinsa kamar
    wani soja awannan daren dai sai bacci barawo
    shine yayi nasarar sace shi daf da asuba. Da
    misalin 8 ta fito ta shiga kitchen kamar kullum
    ta shirya lafiyayyen breakfast ta kawo kan dining
    ta jera tana gamawa ta shiga dakinta tayi
    wanka ta fito tashirya cikin wata body hug baka
    mai dan siririn hannu da wata bakar skirt ta
    matseta sosai ta gyara gashin kanta ya sauko
    har gadon bayanta ta feshe jikinta da turaren
    urban woman tasa wata bakar hula mai gashi ta
    nufi falo tana fitowa ta hangoshi akan dining a
    zaune ya zubawa abincin ido fuskar nan tasa
    tayi mutukar kyau yana sanye da orange colour
    din t. Shirt mai gajeren hannu da blue din jeans
    hannunsa daure da agogo golden colour gaba
    daya falon ya gauraye da kamshin turarensa
    manyan idanuwansa ya dago yafara kallonta
    fuskarta tasha make-up kayan da tasa sunyi
    bala'in matseta kuma sunyi mata kyau abunka
    da farar mace nan da nan yaji ya rude ya nemi
    nutsuwarsa ya rasa tuni hankalinsa ya soma
    neman tashi kallo kawai yake binta dashi dakyar
    ya iya furta pls zo ki hada min tea din,
    ayangance kamar mai tausayin kasa ta tako
    zuwa kan dining din ta dan russuna yaya ina
    kwana acan kasan makoshinsa yace lfy beauty
    MACE GUDA DAYA TILO
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£7⃣

    Tea din ta fara hada masa sai wani shan
    kamshi take shi kuwa lamin yasaki baki sai
    binta da kallo yake sai kace wani soko tana
    gama hadawa ta kawo gabansa ta dire masa ta
    juya zata tafi hannunta taji ya ruko cikin nashi
    jawota yayi ya zaunar da ita akan cinyarshi
    yafara murza yan yatsunta cikin nashi ahankali
    kamar kullum yarr! Taji nan da nan ta tuno da
    yan matansa acikin zuciyarta tace yanzu suma
    haka yake yi musu ko? Wata zuciyar tace mata
    fin haka ma yayi kamar wadda aka tsikara tayi
    zumbur ta mike ta fincike hannunta kallon
    mamaki yabita dashi wai junada meye yake
    damunki ne?. Bata kalleshi ba ta wuce daga
    dining area din falo taje ta zauna ta kunna kallo
    tana nan zaune har ya gama yin break din ya
    taso ya dawo falon ya zauna yana zama ta
    tashi ta shige dakinta tayi zamanta abin duniya
    ya taru yayi masa yawa shima mikewar yayi ya
    nufi side din daddy anan ya iske mummy zama
    yayi suka fara hira babu laifi ya dan jin saukin
    damuwar da yake ciki. Anan ya kusan wuni sai
    da yamma yakoma side dinsu yana shiga ya
    tarar dasu husna suna zaune a falo ita kuma
    junada yajiyo motsinta a kitchen dakinsa
    yashiga yayi wanka yafito cikin ash colour din
    riga da bakin wando kansa tsaye ya shiga
    kitchen hangota yayi tana kaiwa da kawowa
    acikin kitchen din daga ita sai wata yar
    mitsitsiyar shimi ja da dogon wando masha
    Allah yafada acikin zuciyarsa ahankali ya karasa
    daf da ita ya tsaya tana jinsa taki jiyowa ta
    shareshi gyaran murya yayi sannan yace sannu
    da aiki beauty sunan taji har cikin ranta ita dai
    tana son muryarsa shiyasa take son taji yana
    mata magana koda kuwa fada ne jikinta ya
    matso ya ziro hannuwansa ta bayanta yace
    kawo in yanka miki salak din a'a kabarshi
    nagode ta fada cikin wata iriyar murya domin
    gaba daya ya gama rikitata lokaci daya saboda
    duk yabi ya dabaibaye ta ya hanata sakat kafa
    sakar min nauyinka nauyi kuma? Ni wanne nauyi
    gareni? Au kai bakasan kanada nauyi ba? Ni
    banida wani nauyi babu mamaki ma idan akace
    kin fini nauyi uhm anya kuwa zan fika nauyi? To
    ko za agwada ne? A'a ba sai mun gwada ba
    tafada tana girgiza kai hmmm yayi murmushi ke
    kin fiya raki dayawa.
    MACE GUDA DAYA TILO
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£8⃣

    Kin fiya raki da yawa tun yanzu kin fara
    cewa inada nauyi anya kuwa zaki iya naukar
    nauyina? A'a bazan iyaba tayi masa gatse acikin
    zuciyarta kuwa cewa take wadan nan tsiga tsiga
    matan ma suka iya daukar ka balle ni?
    Hannuwan shi ya janye daga jikinta yace natafi
    masallaci ya juya yafita ita kuwa wata ajiyar
    zuciya ta sauke. Tunda ya fita salla bai dawo ba
    sai bayan sallar isha yau falon babu kowa
    mamaki ne ya kamashi to ina suka shiga?
    Dakinta ya nufa ya murda yajishi a kulle yadawo
    nasu hasna shi kuma a bude yake amma basa
    ciki duk yadda akayi suna side din mummy
    yafada acikin zuciyarsa can din ya nufa
    yasamesu sunata hira da mummy amma babu
    junada ganin haka yasa ko zama baiyi ba yafice
    sai yanzu ya gano wato daki ta shiga ta rufe
    kenan dan kar ya bukaci wani abu agurinta tsaki
    yaja yace ni kuwa zan baki mamaki junada in
    dai nacika lamin baxan sake nuna miki bukatata
    akanki ba kan dining yaje ya samu ta shirya
    komai faten dankali da hanta sai salad data
    hada masa domin tasan shi yana son salad
    zama yayi yaci ya koshi sannan ya shiga
    dakinsa wanka yayi abin mamaki hatta ruwan
    wankan ta hada masa murmushin mugunta yayi
    yace yarinya ina tausaya miki cike da damuwa
    yayi baccin wannan rana.
    [3/24, 10:32 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£9⃣

    Washe gari da safe ya tashi yayi wanka ya
    shirya ya fito yauma kamar jiya taci ado tamkar
    baturiya cikin wata doguwar Riga dark brown
    shara shara mai hannun shimi ta tufke gashin
    kanta wanda yake lodi guda ta kame akan kujera
    har cikin zuciyarsa yaji sonta ya ratsashi babu
    karya ta tafi da imaninsa ahankali ya jefeta da
    wani irin kallo wanda shi kadai yasan
    ma'anarsa falon yashiga ya zauna ina kwana
    yaya lamin tace dashi cike da murmushin da
    yake karawa fuskarsa kyau yace lfy lau kawo
    min tea kawai yau babu abinda nake sha'awar
    ci kallonsa tayi nayi maka farfesu fa a'a ki ajiye
    min anjima zanci yanzu fita zanyi tashi tayi taje
    ta hado masa ruwan zafin ta kawo masa kadan
    yasha sama sama yatashi ya kwashi wayoyinsa
    da key din motarsa ya fita lekensa ta farayi ta
    window ga mamakinta sai taga ko side din
    mummy bai kalla ba ya shiga motarsa yafita
    daga gidan to ina ya tafi?? Ta tambayi kanta
    karfa yakoma yawon bin matan da yasaba
    gabanta taji ya fadi ya Allah ka kare wannan
    bawa naka,ka kawar da idonsa daga kan matan
    banza Allah ka dawo min dashi lfy wani irin
    kishine taji yana taso mata agaskiya tana kishin
    lamin sosai domin tasan mijinta ya hadu ta
    kowanne bangare tamkar tauraro yake acikin
    taurari kana ganinsa kaga cikakken bafulatani
    yanayin da taganshi lokacin da yana bacci ne ya
    fado mata hmmm dole yan mata suna rububinsa
    domin kyansa ya isa.
    MACE GUDA DAYA TILO
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£0⃣

    Haka ta zauna sukuku ko tea dinma ita
    takasa sha domin duk a tunaninta yawon neman
    mata ya tafi musamman ma yau da taga ko
    sha'awar taba hannunta bai yi ba, nan ta nemi
    wuri ta zauna tanata sakar zuci ta na nan zaune
    har su husna suka tashi daga barci suka fito
    sukazo suka isketa a falon suka fara kokarin yin
    break ita kuwa hirar da suke yimata sama sama
    take ji domin bata cikin nutsuwa hankalinta
    naga abin sonta lamin ni dai ummi A'isha yar
    kallo ce, tana nan zaune motsi kadan ta kalli
    agogo har 12 tayi ganin bai shigo ba yasa ta
    tashi tashiga kitchen tabar su husna suna kallon
    wani Indian film atashar zee aflam mai suna
    muhabbatien,aiki take amma sam babu walwala
    da sukuni a tattare da ita ahaka ta gama hada
    hadaddiyar fried rice dinta wadda tasha hanta
    da carrots ga cabbage yaji sai kamshi take tayi
    wara wara da ita gwanin sha'awa dan ko ni
    ummi A'isha saida naji yawuna ya tsinke, tana
    gama hada fried rice din ta soya naman zabbi
    tayi masa kykkyawar suya ta tattara komai ta
    zuzzuba a cikin food flask ta kawo kan dining
    tafara jajjerawa su husna dake falo suka fara
    tandar baki hasna ta taso tace Anty me kika
    girka mana ne? Hararta tayi tace mijina nayiwa
    girki ku jira idan yaci ya rage sai ku karashe
    sauran dariya hasna tayi ta koma falon tana
    fadin to bari mu zauna zaman jiransa husna
    dake zaune tana sauraronsu tace ai kema hasna
    nasha fada miki mu tattara mu koma sashen
    mummy amma kika ki gashi nan ai muna ganin
    wariyar launin fata awajensu dariya sukayi
    hasna tace ai Anty tana shagwaba yaya tafi
    sonsa ma akanmu murmushi junada tayi tace ai
    dole dama nafi sonsa tunda matsayinsa yafi
    naku dariya suka yi ita kuwa daki ta shiga tayi
    wanka ta shirya cikin atamfa super kalar ruwan
    kwai ta yiwa fuskarta kwalliya sosai ta kafa
    dauri kamar goggoro ta feshe jikinta da
    turarruka masu dadi tasa sarka fashion golden
    colour ta fito falo lokacin karfe 4 har tayi wuri ta
    nema ta zauna tana jiran gawon shanu, ni dai
    ummi A'isha ina daga gefe ni ma ina sauraron
    zuwan oga lamin.
    Ummi A'isha
    [3/24, 12:34 PM] Ummi A'isha🏻: [3/24, 10:37
    AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO..

    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£1⃣

    Tana nan zaune har 5 tayi tuni su hasna sun
    tafi sashen mummy ita kuwa junada ta cika tayi
    dam kiris ya rage ta fashe, sai 5:30 ya shigo
    gidan tana zaune a falo ya bude ya shigo
    hankalinsa kwance fuskarsa wasai ganin haka
    yasa junada taji ta dada tsarguwa da shi kallo
    bishi da shi babu alamun damuwa ko kadan a
    fuskarsa sallamarsa ce ta katse ta, ta amsa
    fuska babu annuri can nesa da ita yaje ya zauna
    tuni ta gasgata zarginta fuskarsa dauke da
    murmushin keta yace ina su hasna? Kamar ba
    zatayi magana ba tace suna side din mummy
    kallonta yayi kwalliyar tata tayi masifar yi masa
    kyau gamida jan hankalinsa amma bai nuna
    mata hakan ba shi kansa ya san junada first
    class ce asahun kyawawan mata kamar yadda
    yake first class a sahun kyawawan maza
    dagowa yayi yaga ta kafe shi da ido ko kiftawa
    batayi wai lfy kuwa? Ya tambayeta lafiyar ce ta
    kawo haka tafada tana mai ci gaba da kallonsa
    har sai da ta tabbatar da zarginta domin lips
    dinsa taga alamun jan baki ajiki a fusace ta
    mike yabita da kallo ya ce gobe ki shirya za
    muje bauchi banza tayi masa ta shige dakinta
    shi kuwa tashi yayi ya hau kan dining yafara
    kwasar girkin da ta tanadar masa. Ita kuwa
    junada tamkar zata mutu dan kunar rai,
    hankalinta duk yabi ya gama tashi ita kam ya
    zata yiwa lamin ya daina neman matan nan?
    Wata zuciyar tace duk laifinki ne meyasa
    alokacin da yazo miki da bukatarsa baki bashi
    hadin kai ba? Ai da kin amince dashi kin bashi
    kulawa to da babu macen da zata sha gabanki
    awurinsa saboda duk matan da zai yi mu'amula
    dasu awaje babu wacce zata nuna miki kyawun
    halitta, hakika nayi babban kuskure da ban
    amincewa lamin ba lokacin da ya bukaceni ta
    fadi hakan acikin zuciyarta mikewa tayi tace ya
    zama dole na tsaya na gyara kuskure na tunda
    wuri.
    MACE GUDA DAYA TILO
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£2⃣

    Falon ta koma akan dining ta ganoshi yana
    cin abinci yana waya amma bata hango
    fuskarsa saboda ya bata baya hakane ya bata
    damar bude idonta sosai tafara kare masa kallo
    komai nashi mai kyaune ya hadu ta kowanne
    fanni tamkar shi yayi kansa tana nan zaune har
    ya gama cin abincin ya tashi ya shiga dakinsa
    Jim kadan sai gashi ya fito daga shi sai gajeren
    wando kallo 1 tayi masa ta sunkuyar da kanta
    kizo ki zuba min ruwan wanka tun kafin ya
    karasa ta mike a zuciyarta tana cewa ai dole
    kayi wanka dan kai kadai kasan me ka aikata
    bathroom din ta shiga ta hada masa ruwan
    sannan ta fito ba tareda ta kalleshi ba tace na
    zuba maka yawwa thank you taji yafada cikin
    tausasshiyar muryarsa fitowa tayi daga cikin
    dakin ta nufi nata ta fara shirya kayanta acikin
    babbar trolley sai dai acan kasan zuciyarta
    kuma tunanin tafiyar nan da zatayi take anya
    kuwa idan ta tafi bazai samu damar holewarsa
    yanda ya gadama ba? Mts tsaki taja tace nasan
    dai duk tsiyarsa bazai kawo mata gidan nan ba
    tunda su mummy suna nan sai dai yaje hotel da
    wadannan tunane tunanen tagama hada duk
    abinda tasan zata bukata. Washe gari da
    wurwuri ta tashi ta hada breakfast ta gyara
    gidan ta shiga tayi wanka ta fito taci kwalliya
    cikin wani leshi orange tasha kwalliya tayi kyau
    sosai ta fito kamshi ne kawai ke tashi daga
    jikinta tana fitowa ta hangoshi shima har ya
    shirya yafito yana zaune yana cin soyayyen
    dankalin da ta soya masa yayi kyau sosai cikin
    wani lallausan bakin yadi mai tsadar gaske yasa
    hula itama baka agogon hannunsa na azurfa ne
    sai kyalli da walwali yake kamar kullum kamshin
    turaren Phoenix ne ke tashi daga jikinsa kallonsa
    tayi acikin zuciyarta tace Kai dai ko wanne kaya
    kasa sai yayi maka kyau gaka da son kamshi
    kamar me, afili kuwa dan russunawa tayi tace
    ina kwana? Kin tashi lfy? Lfy lau kujera itama
    taja ta zauna ta hada tea tasha agurguje ta
    shiga side din mummy tayi mata sallama tafito
    lokacin suma su hasna sun tashi kayanta ta
    dauko tafito sukayi sallama ta nufi inda yake
    tsaye yana jiranta.
    MACE GUDA DAYA TILO...
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£3⃣

    Wata sabuwar mota katuwa baka taga ya
    dauko yazo gabanta ya tsaya su husna ne suka
    bude mata motar ta shiga yaja suka fita daga
    gidan tana ta dagawa su hasna hannu, kira'ar
    sudais ya kunna cikin suratul Yusuf ya kure A. C
    din cikin motar lumshe idanuwanta tayi tana
    sauraron karatun tana bi acikin zuciyarta kamar
    a mafarki taji shima lamin yana bi ahankali
    mamaki ne ya cikata ashe dai shima
    mahaddacine sai tsabar shagala Allah ya kyauta
    tafada cikin ranta gudu yake sosai tun tana
    tsorata har ta daina dan ta fahimci yanayin
    tukinsa ne haka kafin kace me bacci yayi awon
    gaba da ita kallon fuskarta yayi yaga tana bacci
    wani kayataccen murmushi ya saki junada
    kenan junada zanyi mutukar baki mamaki
    yafada acikin zuciyarsa. Karfe 12 suka isa garin
    bauchi sai da suka shiga cikin gidan sannan ya
    tasheta cikeda mamaki tace har munzo? Eh ga
    zahiri kuwa kin gani fitowa sukayi daga cikin
    motar suka tasamma cikin gidan suna shiga falo
    ta hango ummanta ai da gudu taje ta fada
    kanta ta rungumeta shi dai lamin abinma dariya
    ya bashi sai yau ya yarda junada muguwar
    yarinya ce, dakyar ta daga umman tata suka
    gaisa da lamin nan da nan aka cikasu da kayan
    ciye ciye waya ummanta tayiwa abbansu tafada
    masa zuwansu, office din ya baro yazo suka
    gaisa da lamin, sai da lamin yayi sallar azahar
    sannan yayi musu sallama ya fito biyo shi
    junada tayi tace sai yaushe zan dawo sai kin
    ganni nadawo 2 weeks zakiyi, tace to Allah ya
    kaika lfy amma dan Allah ka rage gudu, har
    cikin ransa yaji dadin maganarta murmushi yayi
    mata yace insha Allah yashiga motar ya tafi.
    [3/24, 10:40 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£4⃣

    Tsayawa tayi har sai da taga fitarsa sannan
    ta shiga gida ta na mai addu'ar Allah ya kaishi
    gida lfy. Wuni sukayi suna hira ita da ummanta
    har Abbanta ya dawo daga office shima suka ci
    gaba dashi,sai bayan sallar isha sannan ta shiga
    dakinta wanda har yanzu yana nan a kintse
    babu abinda aka canja sai kace tana gidan.
    Wanka taje tayi tazo ta shirya cikin rigar
    baccinta ta haye gado, lamin ne ya fado mata
    Allah sarki ko yanzu me yake yi? Ko har yayi
    bacci? Ko kuma kallo yake? Wayarta ta jawo ta
    fara kiran husna ringing 3 ta daga tana fadin
    Allah yabar Antynmu dariya junada tayi sannan
    tace yagida? Gida lfy ya kika tarar da mutan
    gida? Duk lfy ina hasna? Hasna tana falo ni
    kuma na shigo daki, ok ina yayanku? Gashi can
    na hangoshi ta window yana fitowa daga side
    din daddy, wanne irin kaya ne ajikinsa? Body
    hug baka da boxer baki ajiyar zuciya junada
    tayi sannan tace kije kice ina gaidashi da fatan
    ya isa gida lfy to Anty angama, mikewa husna
    tayi ta fita zuwa inda ta hangoshi yana zaune
    acikin wata yar karamar runfa wadda aka
    tanada domin hutawa da wasu yan kujeru aciki
    sai kace a turai sannu yaya yawwa sannu dama
    Anty junada ce tace ince tana gaisheka da fatan
    ka dawo gida lfy? Murmushi yayi sannan yace
    kice ina amsawa sannan kuma na dawo lfy da
    fatan zatayi bacci lfy to tafada ta juya tana cikin
    tafiya junada ta kirata ta daga tafada mata
    sakon murmushi junada tayi tace nagode kigaida
    su mummy ta kashe wayar ko ba komai
    hankalinta ya dan kwanta tunda taji halin da
    yake ciki amma kuma sai ta tsinci kanta da son
    ganinsa a wannan lokaci fatanta daya Allah yasa
    ba da wata manufa ya dawo da ita gida ba.
    MACE GUDA DAYA TILO...
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£5⃣

    Juyi kawai takeyi amma bacci ya kauracewa
    idonta tunanin mijinta ne kawai ke addabarta da
    kyar ta samu bacci ya dauketa. Da safe da
    misalin karfe 10 ta kira husna ta tambayeta ina
    lamin? Murmushi husna tayi tace yana side
    dinku yana bacci inajin bai tashi ba cikeda
    damuwa junada tace dan Allah kije ki gano min
    shi tashi husna tayi ta fita tana ta faman mita ni
    kam ai na shiga uku kuma da haka takarasa
    sashen nasu ta lalleka dakunansa amma baya
    ciki dakin junada ta buda abin mamaki hangoshi
    tayi baje akan gadon junadan yanata sharar
    bacci rufe kofar tayi tajuya ta fita tafara kiran
    junada tana dagawa ta fara bata labarin lamin
    wani dadi junada taji ashe dai yafara damuwa
    da ita yanzu. Abin har ya zamewa husna jiki
    domin kullum junada sai ta kirata ta tambayi
    lamin hatta kalar kayan da yasa sai an fada
    mata kuma sai taji shin ya fita ko bai fita ba da
    haka har tayi sati 1 da zuwa aranar kuma ta tafi
    azare gidan kanwar mamanta mami da niyyar yi
    mata kwana 2 nan da nan mami ta fara yi mata
    dure dure da tsume tsume ita junada abin ma
    har isarta yayi aranta kuwa fadi take ai wanda
    aka yimin a sudan ma har yanzu yana nan
    ajikina kwananta 2 ta dawo gida cikeda kayan
    gyare gyaren da mami ta hado mata. Ranar da
    ta dawo aranar yayunta suka dawo daga
    makaranta Khalid da Amir harda cousin dinsu
    Mahmud wanda shima duk tare suke karatun a
    waje kar kaso kaga murna wurin junada haka
    tashiga cikinsu suka baje ana ta hirar yaushe
    gamo kasancewar ko lokacin bikinta basu samu
    sun dawo gida ba.
    Ummi A'isha
    [3/24, 12:34 PM] Ummi A'isha: [3/24, 10:45 AM]
    Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO

    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£6⃣

    Yanzu tafi jin dadin zaman gidan saboda
    dawowar su Khalid kullum wuni suke suna hira
    amma fa tunanin lamin yana nan makale acikin
    zuciyarta, waya kuwa kullum sai ta kira husna
    taji labarin lamin amma hankalin ta yadan
    kwanta domin kullum yana gida baya fita koda
    wanne lokaci idan ta tambayi husna ya fita sai
    tace a'a yana wurin daddy ko kuma yana side
    din su. Ahaka har hutun nata ya kare husna ce
    takirata take ce mata Anty yaya yace ki shirya
    ranar Saturday zai zo ku tafi domin ranar
    Monday zamu koma sch murmushi tayi to husna
    kice masa zan shirya, nan da nan tafara harhada
    kayanta wuri guda. Hakan kuwa akayi ranar
    Saturday sai gashi wurin karfe 12:30 lokacin da
    ya shigo falon yayyun junada suna zaune hannu
    ya basu suka gaggaisa har umma tafito itama
    ya gaida ta dakin junadan ta leka ta ganta tana
    shiryawa tace to kifito yazo idan kukayi sallah
    kuka ci abinci sai ku tafi to umma ina zuwa inji
    junada tana gama shiryawa ta fito ta sameshi
    zaune a falo yasha waganbari milk colour da
    hula milk colour ya gyara sajensa fuskarsa tayi
    kyau hannunsa ya daura agogon fata milk
    colour gabansa ta karasa tana fadin yaya lamin
    sannu da zuwa amsawa yayi yana kallonta tayi
    kyau sosai cikin bakin material din data sa
    kallon da ya lura Mahmud yana yima ta ne
    yasashi fadin kije ki dauko mayafinki to tafada
    ta tashi tafita. Saida suka ci abinci sukayi
    sallah sannan suka fito da niyyar tafiya Khalid
    ne yayi dariya yace autar umma kin manta
    wayarki awurin mahmud kallon khalid din tayi
    tace wlh naso na manta kuwa hangowa
    mahmud din tayi shida amir suna tahowa tace
    yawwa gashi nan ma shida yaya amir shidai
    lamin yana tsaye baice komai ba har suka
    karaso wurinsu khalid ne yace mahmud ka bawa
    auta wayarta zasu tafi dariya Mahmud din yayi
    yace ai ba ita ta baniba warta nayi dan haka
    nima ba bata zanyi ba tunda lokacin danace ta
    aramin guduwa tayi.
    MACE GUDA DAYA TILO...
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£7⃣

    Guduwa tayi wurin mummy dan haka nima
    bazan bata ba kallon khalid tayi tace yaya
    Khalid dan Allah karbo min wayata, karbo mata
    yayi ya mika mata shi kuma mahmud yaci gaba
    da fadin ai wlh yarinya ba don kin gudu ba da
    sai na murde hannunki na kwace, kallonsa lamin
    yayi cikin kunar rai tuni zuciyarsa tafara tafasa
    motar ya bude yashiga itama shiga tayi ta
    zauna hannu suka fara daga musu amma lamin
    ko kallonsu bai yi ba saboda ransa ya gama
    baci ai nan take ya murtuke fuska idanuwansa
    suka rine sukayi ja acikin ransa fadi yake warta?
    Ya warci waya a hannunta? Yabita ta gudu
    wurin umma? Lallai ashe ma wasa sukayi tunda
    harda su guje guje yayi kyau yafada afili ita dai
    junada tuni ta gama tsurewa saboda bata san
    meya bata masa rai ba ko kadan ba ta zata
    maganganun mahmud sunada nasaba da bacin
    ransa ba shiyasa taja bakinta tayi gum ahaka
    har suka isa garin yola. Yamma lis suka shiga
    gidan amma har yanzu lamin akule yake da ita
    yana parking ko kallonta baiyi ba yafice ya shige
    side dinsu ita dai batasan me tayi masa ba,
    fitowa itama tayi ta kwashi kayanta ta shigar
    cikin falonta sannan tashiga wanka tayi salla ta
    nufi side din mummy tana shiga su husna suka
    taso suka rungumeta cike da zolaya husna tace
    yau nima zan huta da tambaye tambayen da ake
    min hasna tayi caraf ta cafe ai dan an san zaki
    iyane shiyasa aka saki ni da aka san bazan
    iyaba ai kinga ba asaka ni dariya suka saka
    mummy tace kun karata dai masu surutun tsiya
    karasawa junada tayi ta durkusa ta gaidata
    sannan ta tashi takoma side dinta yan rakiyarta
    suna biye da ita abaya.
    MACE GUDA DAYA TILO...
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£8⃣

    Suna shiga ta fada kitchen ta dafa musu
    indomie da kifi ka kawo musu shi kuma lamin ta
    dora masa tasa akan dining, shiru shiru har dare
    yayi bai fito ba yana can acikin dakinsa ita
    kuma tsoron yi masa magana take, har suka
    gama hirarsu suka shiga daki bai fito ba, abin
    yayi mutukar damun junada domin bata son
    bacin ransa ita ba abun taje ta tambayeshi ba
    wata zuciyar tace mata ki bari sai ya huce
    tukunna sai ki tambayeshi inyaso alokacin sai ki
    bashi hakuri gaba kuma sai ki kiyaye da wannan
    shawarar tayi amanna. Washe gari ta tashi ta
    gyaggyara gidanta tayi komai amma girkin data
    ajiyewa lamin yana nan yadda yake bai ko buda
    ba ranta taji ya sosu to shi wannan me nayi
    masa ne? Ta tambayi kanta amma ganin bata
    da amsa yasa ta ci gaba da abinda take. Wasa
    wasa har tayi sati daya da dawowa lamin baici
    abincinta ba asalima ita tun daga ranar da suka
    dawo daga bauchi bata kara saka shi a idanunta
    ba kuma yana gidan, da haka suka koma
    makaranta kullum tana busy bata da lokacin
    kanta gashi tunanin halin da lamin yake ya
    gallabi ruhinta ahaka har sati 3 da dawowarta
    amma lamin ya daina cin abincinta ya daina
    kiranta ta hada masa ruwan wanka tama daina
    ganinsa kwata kwata dan haka sai ta tattara
    zamanta ta mayar side din mummy ita dasu
    hasna bacci ne kawai yake dawo dasu side din
    junada. Yau lecture tayi mata zafi ga test din
    unexpected da wani malami yayi musu ga
    lecture note da aka bayar akace kowa ya siya
    ga ta gaji dan haka sai kawai ta kira wani dan
    department din su wanda ta fahimci yanada
    hankali ta bashi sakon.
    [3/24, 10:49 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO...
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£9⃣

    Tabashi sakon tace dan Allah ya siya mata
    lecture note din ya kawo mata gida cikin
    girmamawa yace hajiya inane gidan naki, kasan
    gidan SSG? Eh tsohon gidansa nasani amma
    ban san sabon gidan da ya koma ba, bakasan
    new government house ba? Cikin sauri yace
    nasani hajiya, to kana zuwa government house
    daga gefen dama ba gefen hagu ba, gefen hagu
    gidan deputy governor ne nagefen dama shine
    namu, wani dan kati ta ciro ta mika masa
    ( visitors card) tace ungo wannan sai ka
    nunawa securities din gidan zasu barka ka shiga
    dan Allah ka kawo min ayau dan karatu nake
    son zanyi to hajiya zanzo insha Allahu ya juya
    yatafi yana ta faman murna domin ko ba komai
    yau zaije gidan SSG wanda ba kowane yake
    shiga ba sai mai kwalli a ido irinsu hawwa jabo
    da Adda Benaxir, ita kuwa junada juyawa tayi ta
    nufi motarta domin yunwa takeji sosai ga tagaji
    su husna kuwa tuni sun dade agida dan tun
    12'suka gama lectures dinsu ganin bata gama
    ba yasa sukayi waya gida aka turo musu driver
    ya daukesu. Tana zuwa gida side din mummy ta
    wuce anan taci abinci tayi salla sannan ta wuce
    sashen ta,takwanta tayi bacci sai wurin 4 ta
    tashi tayi wanka taci kwalliya tayi sallar la'asar
    ta fito ta tafi wurinsu hasna tana fitowa ta
    hango wani daga cikin ma'aikatan gidan da
    kayan sojoji yana dosota yana zuwa ya dan
    rissina yace hajiya kina da visitor yana ina?
    Gashi can awurin second Gate,to ina zuwa ciki
    ta koma jim kadan ta fito ta nufi wurin,wannan
    dan department din nasu ta gani cikin sakin
    fuska tace sannu yawwa sannu hajiya gashi nayi
    miki guda biyar bayan kin taho aka bada sauran
    murmushi tayi tace amma nagode ta karba ta
    mika masa kudi yan dari dari nidai ummi Aisha
    ban san ko nawa bane yawan kudin, cikin
    girmamawa yace nagode nagode hajiya ah nice
    da godiya meye sunanka hajiya sunana lamin
    wani kayataccen murmushi tayi sunan maigida
    nane to hajiya nagode Allah yasaka da alkhairi
    sai anjima ya juya yatafi itama juyowar tayi da
    nufin tafiya side din mummy kawai sai hango
    lamin tayi yana tsaye yafito daga side din daddy
    yana sanye cikin wata body hug coffee colour an
    zana hannu ajiki an rubuta show time da wando
    jeans blue yayi mutukar kyau yana jingine ajikin
    motar daddy ya harde hannuwansa akan kirjinsa
    ashe duk wannan abun da yafaru akan idonsa
    ne.
    MACE GUDA DAYA TILO...
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£0⃣

    Nufuto yayi fuskarsa a daure kamar bai taba
    dariya ba yaja hannun ta bai tsaya ako ina ba
    sai falonsu ya mayar da kofa ya kulle ya zare
    key din, ya kalleta yana ta faman huci waye
    wancan? Cikin tsawa yayi tambayar wadda tayi
    mutukar gigita junada badake nake magana ba?
    Nace waye wancan wanda yazo wurinki? Cikin
    dakewa tace dan ajinmu ne ya kawo min lecture
    notes, wato ke bakida hankali ko? Kula maza
    kikeyi baki san hakkin dake kanki ba ko? Bude
    idonta tayi cikin mamaki tafara kallonsa maza?
    Tafada acikin zuciyarta to ita wanne namiji ta
    kula awaje? Yaci gaba da yayyafin masifa ke na
    lura bakida hankali kamar yadda sauran mazan
    dake kulaki na fuskanci dakikai ne marassa ilmi,
    da aurenki zaki rinka biya wasu shashashu wai
    har kuna wasa saboda tsabar jahilci, cikin tashin
    hankali ta kalleshi tace wa na kula har mukayi
    wasa? Au tambayata ma kike? To wannan
    dakikin dan uwan naki mahmud da yake shi
    jahiline mai kwakwalwar kifi shine zai rinka
    kokawa dake alhalin da aurenki to wlh wannan
    yazama na karshe duk ranar da yasake kulaki
    sai na daure dan iska, sai yanzu junada ta gano
    ma'anar fushin da ya ketayi da ita to amma
    wannan ai fadan rashin gaskiya ne, muryarsa ce
    ta dawo da ita gareshi inma banda tsabar rashin
    tunani tayaya mutum zai tsaya yayi wasa da
    matar da ba tasa ba sai irinsu tsinannu
    gogaggun yan bariki nan da nan junada ranta
    yafara baci da zagin da yake yiwa dan uwanta ai
    wannan cin fuska ne kuma ayanda ta fuskanta
    zuwan wannan dan ajin nasu bai bata masa rai
    sosai ba kamar yadda maganar Mahmud ta bata
    masa rai, kallonsa tafara yi cike da takaici tace
    dan Allah dakata min kar ka kara zagar min dan
    uwa saboda kai xan iya canzaka amma shi
    bazan taba iya canzashi ba domin ahalinmu ne,
    kanata wani ikirarin ina kula maza ba gara ni ba
    kaifa? Tsawa ya daka mata wadda saida taji yan
    hanjin cikinta sun juya oh! Kin fara son maza
    ko? Nace kin fara son maza? Lallai ba laifin ki
    bane laifinane cikin bakin ciki tace eh nafara son
    mazan kai mata nawa ka kawo cikin gidan nan
    kayi fasikanci dasu? Ai ko falon nan da ace
    yanada baki ya isa bada shaida, ni kuwa duk
    kule kulen mazana ban taba kawowa gardi cikin
    gidan nan ba kallonta yafara yi sama da kasa
    haka kikace? Nace haka kikace? To yau za ayita
    ta kare akan wanccan shashan dan uwan naki
    kike gayamin bakar magana? Tabbas kin fara
    son maza dan haka yazame min dole ayanzu na
    dauki mataki.
    Ummi A'isha
    [3/24, 12:34 PM] Ummi A'isha🏻: [3/24, 11:00
    AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO...

    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£1⃣

    Yana fadin haka ya danko gashin kanta ya
    nufi cikin dakinta da ita suna shiga ya cillata
    kan gado ya rufe kofar ya zare key din ya jiyo
    yana ta huci ita kuwa junada duk da haka
    bakinta bai mutu ba fadi take wlh sai dai idan
    kasheni zakayi ka kasheni amma babu wanda ya
    isa ya rabani da dan uwana domin jinina ne
    murmushin takaici yayi yace ai kuwa yanzu
    zakiga jinin naki yarinya belt din jikinsa taga ya
    cire da sauri ta runtse idonta don duk zatonta
    dukanta zaiyi tana nan sankame taji shi ya zo
    kusa da ita ya jefa gado cikin sauri ta bude
    idonta ganinshi tayi dagashi sai gajeren wando
    ai tuni suka fara kokawa ganin bata da nasara
    yasa tafara kurma ihu amma sai dai kash! Babu
    wanda zai jiyota, hakuri tafara bashi dan Allah
    yaya lamin kayi hakuri wlh bazan kara magana
    da kowanne namiji ba murmushin mugunta yayi
    yace wlh yau idan kinga na kyaleki to
    numfashina ne ya yanke amma indai ina
    numfashi to sai na rabaki da abinda kike
    tunkaho dashi daga yau zaki daina kula wani da
    namiji a doron kasa, hannuwanta yahada duka
    ta baya ya rike kafin kace kwabo muryar ta har
    ta disashe tun tana iya ihu har ta dawo bata
    iyawa banda hawaye babu abinda ke zuba a
    idonta, shi kuwa lamin baima san a duniyar da
    yakeba ba saboda gaba daya junada ta gama
    rikitashi duk da dama yana yakinin zai sameta
    haka to amma sai yaga ya sameta fiye da
    tunaninsa. Sai bayan sallar isha'i sannan ya iya
    kyaleta lokacin ko motsi bata iyawa shi kansa
    saida ya tsorata saboda yanayin daya ganta
    gaba daya ta jigata marabar ta da matacce
    numfashi, sai alokacin yaji tausayinta ya darsu
    azuciyarsa shi kansa yasan baiyi mata ta dadin
    rai ba saboda lokacin ransa yagama baci
    afusace yake alhalin kuma bai kamata yabi da
    ita ta haka ba sam bai tausaya mata ba yanda
    yasaba bida yan matansa haka yabida ita alhalin
    kuma yasan akwai banbanci su da ita, ahankali
    ya rungumeta yafara hawaye acikin zuciyar sa
    yace Allah nagode maka da kabani kamilalliyar
    mace hakika nasan wannan rahama ce babba
    kayi min batare da ka duba halayyata ba, duk
    yadda na kasance ina saba maka amma sai ka
    dauko kamilalliyar mace kabani,baka bani
    mazinaciya Irina ba ya Allah nayi maka alkawari
    daga yau bazan kara aikata zina ba har nadawo
    gareka, zan tsaya a iya gonata daka albarkaceni
    da ita.
    MACE GUDA DAYA TILO....
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£2⃣

    Hawaye ne yaci gaba da gudana akan
    kumatunsa na tausayin matarsa, shi kansa
    yasan ta wahala dayawa awa 4 ana abu 1
    ummm tom ummi A'isha dai bata da ta cewa,
    ganin bacci ya dauketa yasa yatashi yashiga
    toilet dinta yayi wanka ya fito haka kawai ya
    samu kansa cikin wani nishadi ai rayuwar aure
    tayi yafada acikin ransa domin tunda yake
    yawon bin mata bai taba tsintar kansa acikin
    yanayin da ya samu kansa yau ba, dakinsa yaje
    ya saka jallabiya yayi sallar magrib da isha
    sannan yafito afalo ya tsinkayo wayoyinsa yana
    dubawa yaga miss called din daddy wurin 5
    murmushi yayi yasan dan bai ganshi a masallaci
    bane shiyasa yakira yaji dalili to amma idan ya
    tambayeshi me zaice? Ai gaskiya da kunya dan
    haka sai kawai ya tura masa txt da cewa kanshi
    ne yake ciwo kuma shine da yasha magani
    bacci ya dauke shi sai yanzu ya tashi, dakin
    junada ya nufa lokacin ta farka tana tuno abinda
    ya faru tsakaninta da lamin dazu bude kofar ta
    ga anyi shine ya shigo daga shi sai gajeren
    wando runtse idonta tayi tafara fadin dan Allah
    yaya lamin kayi hakuri ka kyaleni wlh zan mutu
    ahankali yazo gefen gadon ya zauna yakamo
    hannunta ya rike cikin nashi yafara kama yan
    yatsunta daya bayan daya yana murzawa,
    junada! Taji ya ambaci sunanta saura kiris ta
    sume domin ji tayi duk duniya babu wanda ya
    iya fadar sunanta kamar shi, yaci gaba da cewa
    ki yafe min abinda nayi miki nasan na wahalar
    dake ban biki asannu ba amma dan Allah kiyi
    hakuri kinji hawaye taga yafara bin kumatunsa
    ahankali ta girgiza kanta alamun ya daina kuka
    hannunta ya saki ya tashi yashiga toilet ya
    hada mata ruwan wanka yadawo dakin yace
    tashi kije kiyi wanka, bazan iya tashi ba caraf ya
    dauketa ya kaita toilet din wanka yayi mata ya
    gyarata tsaf sannan yadawo da ita dakin ya
    saka mata doguwar riga sannan ya shimfida
    mata sallaya daga zaune tayi sallolin shi kuma
    ya cire bedsheet din ya shimfida mata wani tana
    idarwa ya cire mata doguwar rigar ya saka mata
    rigar bacci ya dauketa ya dora akan gado yazo
    kusa da ita ya zauna me zan dafa miki nasan
    kina jin yunwa ahankali tace tea kawai zansha
    ka duba kitchen akwai ruwan zafi acikin flask da
    sauri ya mike ya Shiga kitchen din ya hado
    mata tea mai kaurin gaske kamar koko ya kawo
    mata dakyar ta tashi zaune ya fara bata har ta
    shanye sannan ya kwantar da ita ya fita kafin
    yadawo har bacci yayi awon gaba da ita.
    MACE GUDA DAYA TILO..
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£3⃣

    Yana shigowa yaga har bacci ya dauketa
    dan haka kusa da ita ya je yakwanta yashiga
    cikin jikinta, can cikin dare yaji zazzabi ya rufeta
    jikinta yayi zafi zau kamar wuta cikeda
    tausayawa yaja bargo ya rufesu sai dai shi baiyi
    wani baccin kirki ba motsi kadan zai tashi ya
    haskata yaga halin da take sannan zai kwanta
    ana jimawa zai kara tashi da haka har gari ya
    waye shi tun asuba yayi salla amma bai tasheta
    ba gudun kar ya katse mata baccinta sai wurin
    6 sannan ta tashi yana kwance agefenta ta dan
    kalleshi sai taga idanuwansa arufe duk azatonta
    bacci yake dakyar ta iya tashi kamar mai koyon
    tafiya tafara takawa ahankali ya bude idonsa ya
    bita da kallo cikeda tausayawa ahaka yaga ta
    fito ta shimfida sallaya tasa dogon hijabinta har
    kasa zama tayi saboda ba zata iya tsaiwar ba
    kwalla ce yaji ta ciko masa ido yayi saurin
    gogewa ahaka ta idar da sallar ta dawo gadon
    ta kwanta, kanta ya dago ya kwantar akan
    kirjinsa yace sannu junada yaya kike jin jikin
    naki, zazzabi nakeji yana neman rufeni kuma
    kaina sai ciwo yake sannan jijiyoyin jikina jinsu
    nake kamar ana tsintsinka min su, cinyoyina
    kuma kamar ana sassara min gashi sunyi tsami
    kuma sunyi min nauyi,cikin tausayawa yace
    sannu bari naje na nemo miki magani, yana
    fitowa falo yaji ana kwankwasa kofar budewa
    yaje yayi husna da hasna yagani a tsaye yaya
    ina kwana lfy ya akayi? Gurin Anty mukazo, me
    zakuyi mata? Mun jita shiru tun jiyane shiyasa,
    lafiyar ta lau,Ku koma ku shirya mana breakfast
    zan zo na karba yana gama fadin haka ya
    maida kofar ya rufe yashiga dakinsa ya saka
    jallabiya da dogon wando yafito saida yasa key
    ya kulle kofar falon sannan yafita motarsa ya
    dauka ya tafi wani chemist ya siyo mata
    magunguna sannan ya dawo gidan, side din
    mummy ya shiga ya dauko kayan breakfast din
    yashiga side dinsu lokacin har ta tashi daga
    bacci tayi wanka da ruwan dumi ta gaggasa
    jikinta babu laifi ta danji dama dama tayi
    kwalliyar ta cikin wani brown din leshi tana
    zaune a falo ta kunna kallo, yana shigowa ta
    sukwi da kanta kasa bata yarda sun hada ido ba
    gabanta yazo ya ajiye abincin ya zuzzuba mata
    soyayyiyar doya da kwai da farfesun hanta,
    sauko da ita yayi ya dorata akan cinyarsa yafara
    bata abaki gaba daya idonta sunyi jawur
    fuskarta ta kumbura abinka da farar mace sai
    kace sweet choco kawata, ahaka har ta koshi ya
    bata maganin tasha sannan shima ya dan ci
    abincin ya tashi ya shiga dakinta ya gyara mata
    ya share ya kunna turaren wuta yadawo falonma
    ya gyara ya shiga kitchen ya wanke mata
    kwanuka ya share sannan ya dawo falon da
    take,kallo kawai take binsa dashi daga shi sai
    best da gajeren wando.
    [3/24, 11:04 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO...
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£4⃣

    Falon yadawo ya feffesa air freshener yasaka
    turaren wuta bugun kofar da yaji ana yine
    yasashi tashi ya leka su hasna ne cikin shirin
    tafiya makaranta lekowa yayi yace ya akay?
    Yaya dama mun shirya ne shine muka biyowa
    Anty, kuyi tafiyarku ita yau bazata ba sai kun
    dawo kofar ya mayar ya rufe, wunin ranar dai
    bai huta ba dukkan ayyukan gidan shine yayi
    mata har tausayi yabata saboda yanda yaketa
    nan nan da ita gashi yanada lecture amma duk
    ya share yaki zuwa shi ta lafiyar matarsa yake.
    Haka ya rinka bata kulawa har na tsawon sati
    daya lokacin da ya fuskanci ta warware ne
    yafara fita kuma aranar ya kawo mata yan aiki
    guda 3 yace bai yadda tayi kowanne aiki ba in
    banda girki da gyaran dakinsa,wata soyayya mai
    wuyar fadi suke nunawa junansu, su husna kuwa
    tuni sun koma sashen mummy domin abin yafi
    karfinsu agabansu lamin yake kissing din junada
    ko ya rungumeta,yauma suna zaune acikin falo
    dukansu suna kallo ya dawo daga office ko
    kunyar su baiji ba yaje yashige cikin jikin junada
    ahankali ya lalubi bakinta yasaka cikin nashi
    hasna ce tace kinga husna zo mu tafi duk
    lokacin da suke da bukatarmu sa kiramu hakan
    kuwa akayi suka tashi suka tafi wurin mummy,
    ita kuwa junada dama tama manta da suna
    wurin domin ta dade tana kaunar jajayen lips din
    lamin dan suna mutukar burgeta. Ahaka
    rayuwarsu tayi ta tafiya cikin farin ciki
    alokacinne Kausar suka dawo daga kasar
    Uganda ita da Abdulrahman cikinta ya tsufa
    sosai, lokacin itama junada ta soma nata yan
    jinyace jinyacen da zazzabi ganin abin yayi yawa
    yasa lamin yakira mata likita har gida yana
    dubata ya ta tabbatar musu tana dauke da juna
    biyu na wata 2 tuni lamin yafara murna wai
    shine zai haifi dan kanshi, murmushi ya saki mai
    kayatarwa junada tace lfy? Kallonta yayi yace
    abin ne ya burgeni dalibata zata haifa min yara,
    murmushin itama tayi tace ai malamin ne akwai
    iya daukar fansa dariya yayi yajawota jikinsa ya
    rungumeta yace duk cikin friends dina fa ni kadai
    ne nayi auri gashi har zan haihu dariya itama
    tayi tace to ai kayi dabara nasan nice zan rigaka
    tsufa tunda kai namiji ne murmushi yayi ya
    kama hannunta yayi kissing dinsa sannan yace
    no ni yanzu inada 27 ke kinada 21 tare zamu
    tsufa, malami dai ya auri dalibarsa.
    MACE GUDA DAYA TILO....
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£5⃣

    Ahaka ya shagaltar da ita da soyayyarsa mai
    wuyar fahimta. Washe gari kausar ta haifi
    yaronta santalele mai kamada lamin sak dan
    haka ranar suna ma sunan lamin din yayansa
    yasakawa yaron, yanzu rayuwa tayiwa junada
    dadi domin ta fahimci ita kadai ce MACE GUDA
    DAYA TILO acikin zuciyar mijinta yana bata
    dukkan kulawa kuma ahaka yayita tayata renon
    cikinta har ya isa haihuwa ranar da zata haihu
    lamin baya nan dan haka sai dawowa kawai
    yayi yaga ta haifi jariranta masu kama dashi
    sak, su husna kuwa tamkar zasu cinye su don
    so shi kanshi lamin yaran sun shiga ranshi
    dayawa haka akasha shagalin suna inda yaran
    sukaci sunan mahaifinsa da mahaifin junada ana
    kiransu sudais da shurem ansha buduri sosai
    washe garin suna mami kanwar umman junada
    ta tafi da ita bauchi tace sai bayan sunyi arba'in
    zasu dawo lamin kuwa bai so ba dan babu
    yadda zaiyi ne amma baiso sukayi nesa dashi
    ba, ita kuwa Mami tayi hakane domin ta samu
    damar gyara masa ita, duk karshen sati yake
    zuwa bauchi wurinsu da haka har suka cika
    arba'in saida suka dan zazzaga dangi sannan
    suka dawo yola lamin ne yaje dakansa ya
    daukosu yaci gayu cikin wani farin boyel mai
    shegen kyau da tsada idan kaganshi bazaka
    taba cewa yana da mata ba balle har kace ya
    ajiye yara biyu.
    [3/24, 11:08 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA

    DAYA TILO.....
    Na
    UMMI A'ISHA
    ƒ£6⃣

    Haka ya debo su yana cike da doki domin shi
    kansa yasan yayi missing din junada, la'asar lis
    suka karaso gida cike da tsarabar bauchi su
    husna sai murna akeyi shi kuwa lamin alla alla
    yake su kebe shida matarsa domin ya tabbatar
    mata da cewa yayi rashinta. Ahaka suka ci gaba
    da rainon yaransu kuma alokacinne aka sanya
    ranar bikinsu husna zasu auri wasu twins yayan
    Governor din garin zamfara, dan haka suna
    gama karatunsu aka fara bikin junada itace uwar
    biki domin itace akan komai yan biyunta kuwa
    har sunyi wayo sun girma ba adade da bikinsu
    hasna ba ta yayesu lokacin sun cika 1 year.
    Haka suka ci gaba da rayuwarsu cikin farantawa
    juna tareda kyautatawa junansu ayanzu auren
    ramuwar gayya yazama auren soyayya. Yau an
    tashi da sanyi junada ta shirya cikin wani jeans
    da riga body hug ta dora katuwar riga sanyi
    asama ta nufi dakin lamin yana kwance yana
    bacci shida yaransu murmushi tayi ta juya
    tafice. Da yamma yafito cikin wata riga t. Shirt
    green da bakin wando ya isketa afalo tayi kyau
    tamkar wata budurwa ta bayanta yaje ya
    rungemata tattausan hannunta tasa ta shafo
    sumar kansa tace naga kayi kwalliya sai ina?
    Neman aure ai tuni tafara kwalla aure ? Dariya
    yayi yace dauko gyalenki ki rakani da gudunta ta
    dauko ta fita ta sameshi a mota shida yan biyu
    suna jiranta cikin garin yola suka shiga basu
    zame ko ina ba sai state university yola suna
    zuwa yafito yashiga cikin hall din inda dalibai
    sukayi dafifi suna jiransa, test ya rubuta musu
    yana cikin rubutunne yan biyu suka shigo cikin
    hall din dagudu sudais ne agaba shurem ya
    biyoshi cikin muryarsa ta yan yara yace daddy
    help me pls dagudu yazo ya rungume lamin
    cikin sauri lamin ya dagashi sama yana fadin
    wooh! Bai kamaka ba gaba daya yan ajin suka
    sa dariya wasu kuwa mamaki suke yanzu
    wannan malamin dama yana da aure? Sun
    ganshi dan yaro dashi ahaka yagama yi musu
    test din suka nufo gida akan hanyarsu ta
    dawowa ne yakalle junada yace yanzu idan
    akace miki zanyi aure sai ki yarda? Kallonsa
    tayi tace ehh mana murmushi yayi yace to ni
    babu auren da nake nema domin ke kadai kin
    isheni kuma ke kadaice MACE GUDA DAYA TILO
    acikin zuciyata, kwantar da kanta tayi ajikin
    kafadarsa tana cewa na gode mijina.
    Alhamdulillah!
    Anan nakawo karshen labarin MACE GUDA DAYA
    TILO, barayin fasaha kuji tsoron Allah ku daina
    yimana editing din littattafanmu batare da
    izininmu ba, duk wanda ya canza min wannan
    labarin ko ya cire sunana yasa nasa, ko yacire
    number na,ko yayi min editing Allah ya isa ban
    yafe ba.
    Fatan Alkhairi gareki
    Halamcy
    Jinjina ga yan uwana marubuta
    Fatima zarah ( d writer of xarah)
    Kausar m Hassan ( d writer of tsaka mai wuya)
    Serdeyeer ( d writer of miss Aysha)
    Zainab Rogo ( d writer of auren gida)
    Hafsat bounzer ( d writer of rabuwa da masoyi)
    Aysha chuchu ( d writer of Duniyarmu)
    Dorlin choco ( d writerof Aysha Noor)
    Benaxir oumar ( d writer of kalma daya)
    Hawwa jabo ( d writer of wacece ita)
    Maman Khadija ( d writer of ni marainiya ce)
    Maman Nana ( d writer of Mairo)
    Cyama galadima ( d writer of Rayuwar rufaida)
    Bebeelo ( d writer of kaddararmu)
    Humaira ( d writer of samra)
    Uhm! Yau fa abin na marubuta ne, yan uwa
    makaranta kuyi hakuri sai mun hadu a labari
    nagaba mai suna..... Nice taku akoda yaushe
    sunan nawa bai canza ba UMMI AISHA

    @BABA-MONO-HAXOR


    No comments:

    Post a Comment


Pages